Gwamna Ajimobi ya kasa sasanta ’yan majalisar APC biyu
Gwamnan Jihar Oyo Mista Abiola Ajimobi ya kasa sasanta ’yan Majalisar Dokokin Jihar biyu, masu suna Temitope Olatoye mai wakiltar mazabar Lagelu da Abiodun Adigun na mazabar Akinyele ta 2 da magoya bayansu suka kece raini a ranar Larabar makon jiya. ’Yan majalisar biyu suna jayayya ne a kan wanda zai kasance dan takarar kujerar […]
Gwamnan Jihar Oyo Mista Abiola Ajimobi ya kasa sasanta ’yan Majalisar Dokokin Jihar biyu, masu suna Temitope Olatoye mai wakiltar mazabar Lagelu da Abiodun Adigun na mazabar Akinyele ta 2 da magoya bayansu suka kece raini a ranar Larabar makon jiya. ’Yan majalisar biyu suna jayayya ne a kan wanda zai kasance dan takarar kujerar Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar APC a zaben badi daga mazabarsu.
An kaure da fada a tsakanin magoya bayan ’yan majalisar ne a kauyen Ojoo da ke kusa da Ibadan, a lokacin da ake jirar isowar Gwamna Ajimobi wurin taron ganawa da masu sayar da kayan motoci dangane da korafin da suka yi cewa, an yi watsi da su a cikin tafiyar da gwamnatin jihar take yi.
Wakilinmu ya ce, a lokacin da ’yan majalisar suka isa wurin taron da magoya bayansu, sai suka fara yi wa juna wakokin habaici, sannan suka fara lakutar hancin juna da fito da adduna da wukake da sanduna lamarin da ya yi sanadin tarwatsa taron kafin isowar Gwamnan.
A yayin da labarin fadar ya isa ga Gwamna Ajimobi, ya hanzarta aikewa da wasu kusoshin Jam’iyyar APC kan su kwantar da al’amarin kafin ya kazanta.
dan majalisa Abiodun Adigun da aka yi masa raunuka da magoya bayansa sun garzaya zuwa ofishin Gwamnan domin nuna masa abin da ya auku gare su.
Gwamnan wanda ya nuna bakin ciki kan aukuwar fadar ya yi zama da bangarorin biyu a ranar Alhamis a cikin sirri, kuma bayanai sun nuna cewa sulhun bai samu nasara ba, saboda dukan ’yan majalisar sun dage a kan kwannensu na cewa shi ya cancanci tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya daga mazabar tasu.