Gwamna Ajimobi ya shirya wa Hausawa liyafa

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya shirya wata ganawa da liyafar cin abinci ga daruruwan Hausawa magoya bayan jam’iyyar APC, reshen Bodija a birnin Ibadan. Gwamnan wanda yake tare da Uwargidansa Florence Ajimobi, a gidan gwamnati da ke Agodi, ya tunatar da al’ummar Arewa mazauna jihar, muhimmancin zama lafiya a tsakanin jama’a. Ya ce […]

Gwamna Ajimobi ya shirya wa Hausawa liyafa
Gwamna Ajimobi ya shirya wa Hausawa liyafa

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya shirya wata ganawa da liyafar cin abinci ga daruruwan Hausawa magoya bayan jam’iyyar APC, reshen Bodija a birnin Ibadan. Gwamnan wanda yake tare da Uwargidansa Florence Ajimobi, a gidan gwamnati da ke Agodi, ya tunatar da al’ummar Arewa mazauna jihar, muhimmancin zama lafiya a tsakanin jama’a.
Ya ce a cikin shekaru 3 da gwamnatinsa ta yi a kan karaga, ta yi gagarumar nasarar dakile tashe-tashen hankula da ke haifar da hasarar dukiyoyi da rayukan jama’a a jihar. Saboda haka, sai ya nemi bakin nasa da su rungumi wannan shiri da hannu biyu domin amfanin ci gaban jihar da kasa baki daya.
 Dangane da harkokin siyasa, Gwamnan ya nuna farin cikinsa da irin goyon bayan da jam’iyyar APC take samu daga bangaren ’yan Arewa da ke zaune a jihar. Ya yi musu alkawarin share musu hawaye a kan bukatun da suka nemi gwamnati ta yi musu a matsayinsu na ’yan kasa ba tare da nuna musu bambancin kabila ko addini ba.
Gwamna Abiola, wanda ya bayyana sha’awarsa ta sake dawowa bisa kujerarsa a zaben shekarar 2015, ya bukaci al’ummar jihar su yi watsi da siyasar kone-kone da kashe-kashe, su rungumi jam’iyyar APC, wacce ta kwantar da hankulansu tare da sama musu ayyukan ci gabansu.
Ya ce, irin ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samar a cikin shekaru 3 da ta yi tana mulki a jihar, ba a taba yin irinsu a cikin shekaru 8 da gwamnatocin baya suka yi ba. “Ayyukan ci gaba masu inganci da muka yi a cikin manya da kananan garuruwan Jihar Oyo a cikin shekaru 3, a bayyane suke, kowa ya gani da idanunsa”. Inji shi.
 Cikin jawabinsa, Shugaban reshen jam’iyyar APC na Bodija (bangaren Hausawa), Alhaji Adamu Muhammed, wanda sakataren watsa labarai, Alhaji Bello Haruna ya karanta a madadinsa, ya jinjina wa tsare-tsaren gawamnatin ne, musamman a kan tsaron lafiyar jama’a. Ya kawo misali da hanzarta daukar matakin shawo kan rikicin da ya barke a bara tsakanin ‘yan kasuwar Bodija (Hausawa da Yarbawa) wanda Gwamna Ajimobi ya yi maganin al’amarin tun kafin ya kazance. “Saboda haka muke tabbatar da goyon bayanmu ga gwamnati mai adalci kuma, mun kammala shirin kada kuri’unmu ga Gwamna Ajimobi da zai sake dawowa neman hayewa bisa wannan kujera a zaben badi”. Inji shi.
Jim kadan bayan ganawar, wakilinmu ya zanta da Alhaji Bello Haruna, wanda ya ce, “Babban dalilin da ya sa muka fito da iyalanmu domin amsa goron gayyatar Gwamna Ajimobi, shi ne gwamnatocin da suka wuce ba su janyo mu a jiki ba, kamar yadda gwamnatinsa ta yi. Mun fara sanar da Gwamnan bukatunmu da ya yi mana alkawarin zai share mana hawaye, nan ba da dadewa ba. Amfanin da ke cikin wannan tafiya, ba zai tsaya ga Hausawan Bodija kadai ba, zai shafi dukkan ’yan Arewa da ke zaune a Jihar Oyo ne.
 “Daga cikin bukatun da muka mika wa Gwamnan, shi ne kayan gudanar da aikin yakin neman zabe, kamar babban ofishin APC na ’yan Arewa a Bodija da motar tafiye-tafiye domin wayar da kan jama’armu a game da manufar gwamna ga mutanenmu wajen kada masa kuri’unmu a zabe mai zuwa.”