Gwamna Ajimobi ya yi addu’o’i da bikin cika shekaru 64
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya yi bikin addu’o’in cika shekara 64, wanda aka gudanar a filin wasanni na Lekan Salami da ke Ademasingba a Ibadan, babban birnin jihar.A jawabinsa, gwamnan ya ce, “Ina rokon gafara daga dukkan wanda muka saba masa a lokacin da muke gudanar da ayyukanmu, ya yi amfani da wannan […]
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya yi bikin addu’o’in cika shekara 64, wanda aka gudanar a filin wasanni na Lekan Salami da ke Ademasingba a Ibadan, babban birnin jihar.
A jawabinsa, gwamnan ya ce, “Ina rokon gafara daga dukkan wanda muka saba masa a lokacin da muke gudanar da ayyukanmu, ya yi amfani da wannan ranar farin ciki ya yafe mana”.
Gwamnan, wanda yake tare da matarsa da ’ya’yansa a wajen bikin, ya yi alkawarin sadaukar da ragowar rayuwarshi wajen rubanya ayyukan bauta wa jama’a ta yadda zai yi dukkan abun da zai iya domin ganin Jihar Oyo ta ci gaba fiye da yadda take a yanzu.
Ya mika godiyarsa ga al’ummar jihar da suka ba shi damar rike ragamar jagorancinsu. Ya ce, ba zai taba ba su kunya ba, domin, “Da yardar Allah sannan da goyon bayan al’ummar Jihar Oyo ne na kai wannan matsayi. Saboda haka zan ci gaba da gudanar da abubuwan da za su janyo zama lafiya da ci gaban jama’a a wannan jiha.”
Da yawa daga cikin mahalarta bikin sun yi na’am da kalaman gwamnan..
Manyan mutane kamar Sarkin musulmin kasar Yarabawa, Alhaji Abdul’Azeez Arisekola Alao da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi da wakilin Olubadan na Ibadan Oba Samuel Odulana Odugade, Ambasada Olusola Saanu da Cif Kola Daisi da shugabannin addinai da kwamishinoni da ’yan majalisu da shugabannin kananan hukumomi 33 na jihar da dimbin magoya bayan jam’iyar APC ne suka halarci wajen bikin.