Gwamna Al-Makura ya rantsar da sababbin shugabannin Hukumar Zabe ta Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci sababbin mambobin Hukumar Zabe ta Jihar su tabbatar sun gudanar da ayyukansu na shiryawa da gudanar da zabubbukan kananan hukumomin jihar da zai gudana nan gaba cikin gaskiya da rikon amana.  Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne bayan rantsar da sababbin shugabannin hukumar da aka gudanar a […]

Gwamna Al-Makura ya rantsar da sababbin shugabannin Hukumar Zabe ta Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci sababbin mambobin Hukumar Zabe ta Jihar su tabbatar sun gudanar da ayyukansu na shiryawa da gudanar da zabubbukan kananan hukumomin jihar da zai gudana nan gaba cikin gaskiya da rikon amana. 

Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne bayan rantsar da sababbin shugabannin hukumar da aka gudanar a Lafiya. Ya ce ba shakka bayan an dauki lokaci mai tsawo ba tare da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar ba. Al’ummar jihar baki daya suna sa ran su ga an yi shi cikin gaskiya da rikon amana. Saboda haka a cewarsa ya zame wa shugabannin dole su gudanar da ayyukansu yadda suka dace don cimma burin haka ba tare da nuna son kai ko bangaranci ba. 

Gwamnan ya ce tuni gwamnatinsa ta aike wa Majalisar Dokokin Jihar wani kudiri da zai kara wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar baki daya daga shekara biyu zuwa uku. A cewarsa gwamnatinsa ta dauki matakin ne don bai wa shugabannin isasshen lokaci don samar wa al’ummominsu musamman wadanda ke karkara romon dimokuradiyya yadda ake bukata. 

Ya ci gaba da cewa “Ina so in kuma tabbatar muku cewa gwamnatina za ta ci gaba da ba ku cikakken goyon baya da tallafin da ya dace a duk lokacin da bukatar hakan ta taso kuma ba za ta tsoma baki a harkokinku ba don tabbatar da nasarar ayyukanku. Saboda haka ya zame muku dole ku guji nuna bangaranci da son kai a yayin da kuke gudanar da ayyukanku na tabbatar da sahihin zabe wanda za a gudanar a dukan kananan hukumomi 13 da ke jihar nan.” 

A jawabin bon Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar, Mista Henry Omaku ya gode wa Gwamnan game da damar da ya ba su ta bad a gudunmawarsu a wannan bangare inda ya tabbatar da cewa za su yi dukan mai yiwuwa wajen tabbatar da an gudanar da zaben cikin tsari wanda a karshe al’ummar jihar da duniya baki daya za su yaba. 

Sauran abubuwa da aka gudanar a wajen taron sun hada da karbar rantsuwa da sababbin shugabannin suka yi. Idan ba a manta ba a farkon Watan Janairun bana ne Gwamna Umaru Tanko Almakura ya sanar da cewar gwamnatinsa ta yanke shawarar gudanar da zaben kananan hukumomi 13 da ke jihar bayan daukar lokaci ba a yi ba.