Gwamna Al-Makura ya yi alkawarin gyara hanyar da ta hada Agbashi da Benuwai
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce idan aka sake zabensa a matsayin Gwamnan Jihar karo na biyu zai gyara hanyar da ta hada garin Agbashi fadar yankin raya kasa na Ekye da Jihar Benuwai. Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne bayan ya mika sandar sarauta ta daukaka martabar Sarkin Agbashi (Otushowo na Agbashi) […]
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce idan aka sake zabensa a matsayin Gwamnan Jihar karo na biyu zai gyara hanyar da ta hada garin Agbashi fadar yankin raya kasa na Ekye da Jihar Benuwai. Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne bayan ya mika sandar sarauta ta daukaka martabar Sarkin Agbashi (Otushowo na Agbashi) Mista Moses Alade daga Sarki Mai daraja na uku zuwa na mai daraja na biyu a garin Agbashi a ci gaba da mika sandunan sarauta ga sarakunan gargajiyar jihar da yake yi. Gwamnan ya ce ya zame masa dole ya gyara hanyoyin idan aka yi la’akari da muhimmancinsu ga al’ummar Agbashi da kewayenta. Ya taya Sarkin murnar daukaka matsayinsa, kuma ya yaba masa wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummarsa.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar yankin su ci gaba da yin biyayya ga Sarkin don ba shi damar ci gaba da hada kansu, kuma ya shawarce su da su tabbatar sun karbi katin zabe don ba su damar kada kuri’unsu ga Jam’iyyar APC wadda ya bayyana a matsayin mai adalci a lokacin zabe mai zuwa don ci gaba da samar musu da abubuwan more rayuwa.
A jawabin Kwamishinan kananan Hukumomi da Harkokin Masauratu na Jihar, Muhammed dan’azumi ya yaba wa Gwamna Al-Makura kan wannan karamci da ya yi wa Sarkin da sauran sarakunan jihar inda ya ce hakan zai kara musu muhimmanci.
A jawabin godiya Mai martaba Sarkin Agbashi Mista Moses ya nuna farin cikinsa inda ya jinjina wa Gwamna Al-Makura dangane da karamcin,kuma ya yi alkawari ci gaba da hada kan al’ummar yankinsa don tabbatar da zaman lafiya da tahimtar juna. Ya kara da ce har idan Gwamnan ya cika alkawarinsa na gyara hanyoyi za su taimaka nesa wajen rage matsalolin sufuri da al’ummar yankin ke fuskanta da dadewa.