Gwamna Atiku Bagudu ya ciri tuta a cikin Gwamnonin Najeriya –Sani Dododo
Ya kake ganin mulkin Sanata Atiku Bagudu a cikin shekara biyu da suka gabata? Dukan godiya ta tabbata ga Allah wanda mulki da iko da rahamarSa suka game duniya baki daya. Salati da sallama ga ma’aikin Allah Annabin Rahama Muhammadu (S.A.W). Na ji dadin wannan tambaya, ganin cewa gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu ta yi shekara […]
Ya kake ganin mulkin Sanata Atiku Bagudu a cikin shekara biyu da suka gabata?
Dukan godiya ta tabbata ga Allah wanda mulki da iko da rahamarSa suka game duniya baki daya. Salati da sallama ga ma’aikin Allah Annabin Rahama Muhammadu (S.A.W). Na ji dadin wannan tambaya, ganin cewa gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu ta yi shekara biyu da wasu watanni.
Hakikan dukanin al’ummar Jihar Kebbi sun san yanzu sun samu gwamna mai sauraren matsalolinsu da kuma jin korafe-korafensu.
Wasu na cewa Gwamna Atiku ya cika kokawa kan cewa ya gaji tulin matsaloli, ya kake ganin wannan al’amari?
Gaskiya ne ya gaji matsaloli masu dimbin yawa kuma dole ne duk wata gwamnati da ta zo ta bayyana takaicinta kan hakan. Wannan ya shafi tattalin arziki da walwala da kuma tsaro. A Jihar Kebbi, babbar matsalarmu ita ce ta lalacewar sha’anin kasuwanci da tarbiyyar matasa da kuma rashin aikin yi da watsi da harkokin noma. Wadannan sune muhimman batutuwan da muke ganin yanzu ana bai wa muhimmanci cikin shekara biyu da watanni, ana kokarin shawo kansu da kuma magance su, ta hanyar sanya wadanda suke da ruwa da tsaki a ciki domin komai ya tafi dai-dai don cigaban al’ummar Jihar Kebbi.
Ya kake kallon gwamnatin ta fuskar tallafawa jama’a da samar da ababen more rayuwa?
Idan za a yi wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu adalci, dole ne ka yaba masa don tsamo wannan jihar daga tsohuwar hanyar da yan’ siyasa suka sanya ta a kan dole komai sai dasu, kuma dole sai yadda suke so.
Na tabbata yana kamanta adalci don kuwa duk da sanyin halinsa ya nuna cewa shi mutum ne wanda ya san abin da yake yi. Na tabbata Gwamna Atiku Bagudu kamar yadda kowa ya sani mutumen kirki ne mai son bin ka’ida da kuma aikata gaskiya da adalci a lamuran yau da kullum.
Wannan yana daga cikin dalilai da ya sanya ya yi fice tun shigarsa siyasa, kuma har Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi Shugaban manoman Najeriya.
Wasu na ganin Gwammna Atiku Bagudu bai aiwatar da wani abin a zo a gani ba, cikin shekarun da ya yi yana mulkin Jihar Kebbi. Me za ka ce?
Abin a zo a gani da Gwamna Atiku Bagudu ya yi wa al’ummar Jihar Kebbi ne ya sa mutanen kwarai suka bar Jam’iyyar PDP suka koma APC, wadanda suka rage a PDP sai dai bara gurbi. Wadansu daga cikin ayyukan da Gwamna Atiku Bagudu ya aiwatar sun kunshi magance matsalar rashin tsabta da ta addabi Babban Birnin jiha, da kuma farfado da gyara tsarin ilimi, da gyaran wutar lantarki da sayo tiransifomomi guda 180 don kara inganta wutar lantarki. Ya kuma biya ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi kudin hutunsu, ana kuma biyan albashi a kan kari tun daga 24 ga wata.
Kuma ko a kwanan nan ya ware Naira biliyan bakwai domin a biya ‘yan fensho, ya kuma ajiye Biliyan daya domin biya wa dalibai kudin makaranta, ya kuma gayyato likitoci daga aasar Amurka domin duba marassa lafiya a duk fadin jihar kuma kyauta.
Kuma tunda aka kirkiro ma’aikatar bayar da agajin gaggawa, ba a taba samun gwamnan da ya kula da ma’aikatar ba kamar Atiku Bagudu. A kullum cikin bayar da agajin gaggawa hukumar take.
Haka kuma ya gina hanyoyin mota a kananan hukumomin Zuru, Yauri, Koko, Augie, Bunza, Maiyama, Arewa, Kalgo, Danko-Wasagu, Dandi da kuma Babban Birnin jiha, inda ya gina hanyoyi sama da 20.
Ba nan Gwamna Atiku kawai ya tsaya ba, koda ya zo ya cimma gwamnatin PDP ta bar bashin kudin makaranta na ‘yan gaba da sakandare da jami’oi na kasashen waje, amma yanzu cikin yardar Allah duk ya biya ba tare da wani bata lokaci ba.
Sannan ga bai wa ma’aikatata ta bayar da agajin gaggawa kudin tafiyar da harkokin yau da kullum na ofis, sabanin waccan gwamnati da ta gabata. Haka ma tun hawarsa mulki, Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da fifiko ga nemo hanyoyin shawara don inganta tarbiyyar matasa da kuma kyautata wa al’umma tare da hana satar dukiyar kananan Hukumomi da biyan hakkokin ma’aikata a kan ka’ida, da kuma ba ma’aikata damar zuwa karo ilimi da sanin makaman aiki.
Amma wasu na fadin sun gaji da gafara sa, basu ga kaho ba. Menene martanin ka a kan haka?
Tabbas akwai masu wannan ikirarin, amma bari in yi tsokaci ga wadanda suke cewa basu san inda ya nufa ba, ya kamata mutane su kalli gwamnatin yanzu da wadda ta gabata. Gwamnatin da ta gabata ta ce ta bar biliyoyin kudi a cikn lalitar gwamnati, kuma ba a binta wani bashi mai yawa, amma sai gashi a binciken da Gwamna Atiku Bagudu ya yi, ya gano cewa Jihar Kebbi dankare take da bashi na ‘yan fansho da ma’aikata da kudin ‘yan makaranta, tun daga sakandare har zuwa jami’oi.
Ina kira ga al’ummar Jihar Kebbi su ba Gwamnatin Jihar Kebbi da Gwamnatin Tarayya cikakken goyon baya domin su sauka nauyin da ke kansu.