Gwamna Badaru a binciki wadanda suka sauya sheka – Aminu Jahun

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jigawa da shiyyar Arewa Alhaji Aminu Jahun ya nemi Gwamnan Jihar, Alhaji Badaru Abubakar ya yi hattara da ’yan PDP da suka koma APC, inda ya ce, ‘ba ’ya’yan goyo ba ne.Aminu Jahun ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Larabar da ta […]

Gwamna Badaru a binciki wadanda suka sauya sheka – Aminu Jahun
Gwamna Badaru a binciki wadanda suka sauya sheka – Aminu Jahun

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jigawa da shiyyar Arewa Alhaji Aminu Jahun ya nemi Gwamnan Jihar, Alhaji Badaru Abubakar ya yi hattara da ’yan PDP da suka koma APC, inda ya ce, ‘ba ’ya’yan goyo ba ne.
Aminu Jahun ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata a harabar kotu lokacin da suka je yin belin Shugaban karamar Hukumar Jahun.
“Wadanda suka sauya shekar zuwa Jam’iyyar APC dama can a cikin PDP ba su da kowa, ba su taba cin zabe a mazabarsu ba. Kuma ba su da wani tasiri, ’yan baranda ne a siyasar Jigawa; ’yan a fasa ne, kowa ya rasa ne. Don haka Gwamna Badaru ya tsaya, ya yi karatun ta natsu. Domin abin da ’ya ci Doma ba zai bar Awai ba,” inji shi. Ya ce, yadda suka  yi wa mai gidansu tsohon Gwamna Sule Lamido, suka ci amanarsa, shi ma ya rubuta ya ajiye, ba jimawa za su ci amanarsa.
Ya roki Gwamna Badaru ya mayar da hankali wajen gina matasa ya sanya su a cikin harkokin gwamnatinsa ya tsaya ya gina mutanensa domin ba ya da kowa a siyasar Jihar Jigawa.
Ya shawarci Gwamna Badaru ya daina yarda da ’yan rudun siyasa maciya amanar jama’a domin wadanda suka sauya shekar, ba ma su kishin kasa ba ne ba su da akidar siyasa a zuciyarsu.
“Wallahi wadanda suka koma  APC sun fada cikinta ne saboda suna bakin ciki, saboda su kawo wa Gwamna Badaru cikas a cikin tafiyarsa, a lokacin zabe mai zuwa a shekarar 2019,” inji shi.