Gwamna Badaru ya ba matasa kayan sana’ar aikin gona kyauta a Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya ce mahassada a Najeriya sun kusa jin kunya, domin Shugaba Buhari ya kusa dawowa domin ya sami sauki soasi. Haka kuma ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya na yi wa ‘yan Jahar Jigawa fatan alkairi saboda ya sami labarin irin addu’ar da suka rika yi masa da kuma […]

Gwamna Badaru ya ba matasa kayan sana’ar aikin gona kyauta a Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya ce mahassada a Najeriya sun kusa jin kunya, domin Shugaba Buhari ya kusa dawowa domin ya sami sauki soasi. Haka kuma ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya na yi wa ‘yan Jahar Jigawa fatan alkairi saboda ya sami labarin irin addu’ar da suka rika yi masa da kuma azumin da suka dauka domin neman lafiyarsa.

Gwamna Badaru ya fadi haka ne a wajen bikin baiwa matasa tallafin kayan sana’ar aikin gona, mata da matasa da aka yi a dandalin masu hidimar kasa dake Fanisau a ranar Talatar da ta gabata.

Ya kara da cewar duk Najeriya yanzu babu jahar da take kasa biyan ma’aikata albashi duk da matsalar karayar tattalin arziki da tsohuwar gwamnatin Najeriya ta jefa kasar nan a ciki, domin a baya an sha bakar wahala wajen kasa biyan albashi a wasu jihohin, amma yanzu an wuce wannan mataki sai dai kananan matsaloli.

Da ya juya wajen wadanda gwamnatin ta baiwa kayan tallafin sana’ar na motoci da babura da kuma maganguna domin bude dakunan magani da asibitocin dabbobi a jahar, ya shawarce su da su rike dukiyar da aka ba su da amana, domin idan sun alkinta wasu ma su amfana anan gaba.

Gwamna Badaru ya kara da cewar koda matsalar mai za ta yi tsamari a kasar nan, Jahar Jigawa ba zata jikkata ba daga matsalar tattalin arzikin kasa muddin matasa suka dogara kuma suka rike harkar noma da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, tare da taimakon gwamnatin Jigawa domin akwai bukatar matasa su rungumi harkar noma da muhimmanci saboda lokaci ya yi na inganta harkar noma, saboda nan gaba kadan kasuwar mai za ta mutu a kasashen duniya.

Amma a gefe guda wasu matasa sun koka tare yin korafin cewar gwamnatin jahar ba ta tafiya da su, alhalin sun bautawa jam’iyya, maimakon a debe su a taimaka masu, amma ba sa cikin wadanda suke amfana daga irin abubuwan alkairi da gwamnatin ta ke yi. Daya daga cikin matasan, Muhammad Sani Garko Kiyawa, ya ce idan Badaru bai tsaya ya yi gyara a cikin tafiyar ba, su ma za su balle daga tafiyar zuwa wata jam’iyyar, domin ba a yi da matasa ko kadan. “Ita wannan gwamnatin ba ta tafiya da wadanda suka sha wuyarta sai da baki wadanda ma ba su da wata alaka, su ne kawai su ke jin dadinta, bayan mu muka sha wahala, to hakan ba zai yiwu ba, kura da shan bugu gardi da amshe dala,” a cewarsa.