Gwamna Badaru ya nemi afuwar ‘yan Jigawa
“abubuwa da yawa sun faru a lokacin zaben fidda gwani, wani yana sane wani kuma bai sani ba, amma duk na tattara na dauki nauyin. Allah Ya nuna min isahara a kan zaben fidda gwani da aka yi, domin akwai wadanda na so su zama, amma ba su samu ba, kuma akwai wadanda ban so […]
Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa
“abubuwa da yawa sun faru a lokacin zaben fidda gwani, wani yana sane wani kuma bai sani ba, amma duk na tattara na dauki nauyin. Allah Ya nuna min isahara a kan zaben fidda gwani da aka yi, domin akwai wadanda na so su zama, amma ba su samu ba, kuma akwai wadanda ban so su zama ba, kuma sun zama. Saboda haka ina rokon wadanda na batawa su yafe min.
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar a ranar Juma’ar da ta gabata. Gwamnan ya fadi haka a wajan taron sasanto da ya yi da magoya bayansa wadanda aka batawa a lokacin zaben fidda gwani da ya gabata.
Taron da aka yi a cibiyar horar da ma’aikata dake shedikwatar Jigawa Man Power. Badaru ya nuna farin cikinsa yadda ya ga mutane irinsu Batista Ruba da Danladi Auyo da Tijjani Gaya, ya ce dawowarsu cikin tafiyar APC al’amari ne da ya burge kowa, saboda yadda suka nuna kishin jahar da kuma sa cigaban jahar a gaba.
Gwamna Badaru ya ci gaba da cewa, “Idan muka yi hakuri da junanmu zamu sami dorewar zaman lafiya da cigaba, dan kowa yana bukatar kowa a cikinmu. A matsayinsa na shugaba a yayin wannan zaman na ga mutane wadanda aka batawa, saboda haka ina baiwa wadanda aka batawa hakuri, su yi hakuri.
A karshe Gwamna Badaru ya kafa kwamatin mutane 20 a kowace mazabar sanata wadanda zasu jagoranci yin sasanto da duk wanda aka batawa, sannan aka baiwa kwamatin wa’adin mako biyu ya gabatar da bayanansa ga gwamnati.
Ya kuma bukaci duk ’yan kwamatin su tabbatar sun bi duk wadanda aka batawa gidajansu a basu hakuri, kuma duk wanda bai gamsu ba ya ce sai ni da kaina yake bukatar na bashi hakuri na yarda, kowaye ya zo zan ba shi hakuri a cewarsa.
Gwamna Badaru ya kara da cewar “na san an yi mani hakuri iyakacin hakuri, kuma na san wasu daga cikin wadanda aka batawa din suna da bukatar taimako, amma saboda abubuwa sun yi mana yawa mun yi wa mutane alkawura, wasu mun cika wasu mun manta, dan haka ina kara bada hakuri, na yi maku alkawarin zan gyara inda na yi kuskure,” inji shi.