Gwamna Bagudu shugaba ne mai daukar shawara da aiki da ita – danmalikin Kebbi
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Najeriya da aka samu canjin akalar gwamnati daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, sai dai har yanzu wadansu mutane na ganin babu wani bambanci a tsakanin tsohuwar gwamnatin da ta shude da wadda take bisa mulki a yanzu, wadansu ma na cewa gwamma jiya da yau. Sai dai Alhaji […]
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Najeriya da aka samu canjin akalar gwamnati daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, sai dai har yanzu wadansu mutane na ganin babu wani bambanci a tsakanin tsohuwar gwamnatin da ta shude da wadda take bisa mulki a yanzu, wadansu ma na cewa gwamma jiya da yau. Sai dai Alhaji Musa Abubakar danmalikin Kebbi, jigo a Jam’iyyar APC kuma ma’ajinta na jihar, a hirarsa da wakilinmu ya bayyana cewa a yanzu jihar ta samu hazikin Gwamna da yake sauraren shawara tare da aiki da ita domin ciyar da jihar gaba:
Yaya kake ganin kamun ludayin wannan gwamnati a shekara daya na Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a Jihar Kebbi?
Na ji dadin wannan tambaya, wannan gwamnati ta Mai girma Sanata Abubakar Atiku Bagudu ba ta dade da fara aiki ba, tana cikin cika shekara daya daga cikin shekara hudu na zangonta na farko. Wata 12 daga cikin wata 48 sun yi kadan aj gano ko a yanke hukunci a kan lamarin mulki da ayyukan raya kasa na kowace gwamnati. Amma kuma duk da haka hakika jama’ar Jihar Kebbi sun san yanzu sun samu gwamnati mai sauraren matsalolin da suke addabarsu shekaru aru-aru da kuma magance su da kuma jin koke-kokensu don daukar matakin da ya dace a kai.
Wasu na ganin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bai aiwatar da wani abin a zo a gani ba cikin shekara daya da yayi yana mulki, me za ka ce?
Ba haka abin yake ba, idan mutane suka lura akwai ayyukan da yake aiwatar da su, amma ba kai-tsaye za a iya ganin amfaninsu yanzu ba, domin sukan dauki lokaci, wasu daga cikin ayyukan da Gwamna Atiku Bagudu ya aiwatar sun kunshi tsabtace babban birnin jihar da kuma farfadowa da gyara tsarin ilimi da gyara wutar lantarki, ya zama awa 24 ba a dauke wuta da kuma sayo taransfomomi 200 domin kara inganta wutar lantarki, ya kuma biya ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi tun daga matakin farko har zuwa karshe kudin hutunsu, ana kuma biyan albashi a kan kari tun daga 25 ga kowane wata. Ba nan Gwamna Atiku ya tsaya ba, ko da ya zo ya cimma bashi na ba ’yan makarantar sakandare abinci sama da Naira biliyan biyu da kuma bashin kudin ’yan makaranta na gaba da sakandare da jami’o’i amma duk ya biya, da kuma biyan kudin fansho da aka fara rage wa wadanda suka yi ritaya da kuma bai wa ma’aikatu kudin tafiyar da harkokin yau da kullum, sabanin gwamnatin da ta gabata. In muka koma ta bangaren hanyoyi, Gwamna ya giggina sababbin hanyoyi a Birnin Kebbi babban birnin jihar da kuma Yawuri ya kuma gyara hanyar nan da ta lalace wadda ta tashi daga garin Dabai Mahuta zuwa Koko. Kuma Jihar Kebbi ita ce kan gaba a duk fadin Najeriya wajen noman shinkafa, jama’a sun shaida sun gani domin har Shugaban kasa Muhammadu Buhari yazo ya kaddamar da noman rani na shinkafa da alkama, ka ga wannan duk yana cikin kokarin da Mai girma Gwamna Atiku ya yi a cikin shekara daya.
Akwai sake tayar da komadar tatalin arziki wajen yin yarjejeniya da gwamnatin Jihar Legas domin gina kasuwar shanu da kuma gyara nama ana kai wa Jihar Legas. Ta kuma jawo manyan ’yan kasuwarmu su shigo a yi da su. Haka Gwamna Bagudu ya bayar da fiffiko ga nemo hanyoyin shawara don inganta tarbiyyar matasa da kuma kyautata wa al’umma tare da hana satar dukiyar kananan hukumomi da biyan hakkokin ma’aikata a kan lokaci. Na tabbata Gwamna Atiku Bagudu kamar yadda kowa ya sani dattijo ne a ayyukansa da kalamansa, mutum ne mai son bin ka’ida da yin gaskiya da adalci a al’amuransa, wannan na daga cikin dalilin da ya sa ya yi fice tun lokacin shigarsa siyasa, Don haka yana da kalubale mai yawa da ke bukatar a yi masa addu’a da fatan alheri don samun nasarar ciyar da wannan jiha tamu gaba.
Wadansu na fadin sun gaji da gafara sa, ba su ga kaho ba, me za ka ce?
Akwai masu wannan ikirarin, amma bari in yi tsokaci ga wadanda suke cewa ba su san inda ya nufa ba, ya kamata mutane su kalli gwamnatin yanzu da wadda ta gabata. Gwamnatin da ta gabata ta ce ta bar biliyoyin Naira a cikin asusun gwamnati, kuma ba a bin ta wani bashi mai yawa. Sai ga shi a binciken da Gwamna Atiku Bagudu ya yi ya gano cewa Jihar Kebbi dankare take da ba shi na ’yan fensho da na ma’aikata da kudin ’yan makaranta tun daga sakandare har zuwa jami’o’i da na ’yan kwangila, sannan tsohuwar gwamnatin ta yi awon gaba da kudin kananan hukumomi na gina filin jirgin sama da kudaden (SURE-P) na tallafin man fetur da kuma shinkafar da ta sayo da kudin SURE-P.
Wadansu na cewa kullum Gwamna Atiku yana kukan ya gaji matsaloli, yaya kake ganin wanna al’amari?
Dole ne duk wata gwamnatin da ta zo za a iya bayyana hakan, cewa akwai wata matsala da take addabar al’umma da ta gada daga gwamnatin da ta shude. Wannan ya shafi tattalin arziki da walwala da kuma tsaro a Jihar Kebbi, manayan matsalolinmu su ne na lalacewar harkar kasuwanci da tarbiyyar matasa da rashin aikin yi da watsi da harkokin noma. Wadannan su ne manyan batutuwa da muke ganin yanzu ana bai wa muhimmanci cikin kankanen lokaci, ana kokarin shawo kansu da kuma magance su ta hanyar sanya wadanda suke da ruwa da tsaki a ciki domin komai ya tafi daidai.
Yaya kake kallon gwamnatin ta fuskar tallafa wa jama’a da samar da ababen more rayuwa?
Idan za ka yi wa Gwamna Atiku Bagudu adalci dole ne ka ba shi dama na ya fahimci abin da ya tarar da kuma tsara hanyoyin da suka dace don tsamo wannan jihar daga tsohuwar hanyar da ’yan siyasa suka sanya ta, ta ala dole komai sai an yi da su, kuma dole komai sai yadda suke so a yi. Huldata da Gwamna ta gaskiya ce, don kuwa tabbas abin da na zaba na tabbata zai yi mana adalci domin duk da sanyin halinsa, ya nuna mutum ne wanda ya san abin da yake yi da kuma aikata ayyukan ci gaba a wannan jiha.