Gwamna Bagudu zai bai wa kananan hukumomin Kebbi dama – Diggi

Alhaji Umaru Namashaya Diggi, ya na daya daga cikin sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi a Jihar Kebbi karkashin APC. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana na cewa Gwamna Bagudu zai bai wa kananan hukumomin jihar dama:   Aminiya: Me yasa ka bar mukamin jami’in alhazzai ka tsunduma  harakar siyasa? Alhaji Umaru Namashaya Diggi:  Na ko […]

Gwamna Bagudu zai bai wa kananan hukumomin Kebbi dama – Diggi

Alhaji Umaru Namashaya Diggi, ya na daya daga cikin sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi a Jihar Kebbi karkashin APC. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana na cewa Gwamna Bagudu zai bai wa kananan hukumomin jihar dama:

 

Aminiya: Me yasa ka bar mukamin jami’in alhazzai ka tsunduma  harakar siyasa?

Alhaji Umaru Namashaya Diggi:  Na ko ji dadin wannan tambaya, abinda yasa na bar kujerar jami’in alhazai na karamar hukumar Kalgo saboda na ce kada a zabi Jonathan, shi yasa aka cire ni, wannan shi ne ya karfafa mani tsunduma cikin harkar siyasa, ya kuma karfafa mani gwiwar fitowa takara, shi ne domin in ba da tawa gudumuwar wajen bunkasa karamar hukumar Kalgo da Jihar Kebbi baki daya. Kuma a matsayina mai akida, domin in karfafa wa ‘yan’uwanmu matasa gwiwa saboda nan gaba mulki zai dawo hannun matasa.

 

Aminiya: Wadanne kudurori kake da su ga wannan karamar hukumar ta Kalgo? 

Diggi: To a takaice ina da kudurori biyar ga wannan karamar hukuma, na farko shi ne kamar yadda muka sani ne cewa duk wani dan Kalgo, babban abinda ya dogara da shi, shine noma. Don haka ina kudurin idan Allah Ya yarda za mu bunkasa harkokin noma a   Kalgo, da yarda Allah za mu cire siyasa kan harkar takin zamani, domin shi manomi abinda yake bukata shi ne a ba shi taki da ingantaccen iri a lokacin da ya dace noman rani ko na damana.

Haka za mu karfafa wa masu kudinmu gwiwa su sanya hannun jari a harkar samar da kamfanonin sarrafa amfanin gona a wannan yanki. Har ila yau zamu sanya su su sa hannu a wajen gwamnatin Kebbi wajen kawo injinan aikin gona irin na zamani a wannan yanki. Sannan akwai maganar ilimi mun san cewa duk wata al’umma da ta samu cigaba a duniya, za a samu cewa ilimi ne jigon wannan ci gaba da ta samu, don haka zamu yi kokari mu kyautata harkokin ilimi a wannan karamar hukuma tun daga makarantun furamare.

Akwai maganar harkokin kiwon lafiya, zamu tabbatar cewa mun inganta asibitocin karamar hukumar, haka ga maganar ruwan sha musamman a lokacin rani. Koda yake a lokacin da nike rike da kujerar kantoman karamar hukuma yawancin injinan da ke ba ruwa da rijiyoyin burtsatse da masu amfani da hasken rana duk na gyara su, sannan yanzu za mu giggina wadansu sabbi ga inda muka ga ya dace ayi.

Bugu da kari zamu bunkasa harkokin kiwo kuma za mu yi kokarin bunkasa harkokin kasuwanci a karamar hukumar kuma kuma a kwanan nan ba da dadewa ba zamu sayo kekunan dunki 300 wanda zamu rabawa mata da matasa domin rage zaman banza a cikin al’umma.

 

Aminiya: Me za kace kan zargin da ake yi wa gwamnoni na danne kananan hukumomi tare da hana su yancin gudanar da ayyukansu?

Diggi: Tsakani da Allah wannan babbar matsala ce, amma mu anan Jihar Kebbi mun gode Allah, domin ko a lokacin da muke kantomomi gwamna Bagudu ya na ba mu kudaden gudanar da ayyuka a kananan hukumominmu, ballantana ma yanzu da muke zababbu, kuma ko da muke yakin neman zabe gwamna na fada cewa zai ba shugabannin kananan hukumomin dama, domin su yi wa jama’arsu ayyuka na cigaba domin suke kusa da jama’a.

 

Aminiya: Wane kira ko sako gareka zuwa ga al’ummar Kalgo baki daya?

Diggi: To sakona ga al’ummar Kalgo shine na farko zuwa ga manoman da aka ba bashin noma tun shekaru biyu da suka gabata, da su hanzarta biyan bashin da aka ba su, su maida domin a samu a ba wadansu su ma su amfana, sakona na biyu shi ne al’ummar Kalgo su bai wa Gwannan Badugu cikkaken goyon baya domin ya kai ga gaci. Sannan shi ma ya cigaba da da kulawa da al’umma jihar Kebbi kamar yadda ya keyi, da wanda ya zabe shi da wanda bai zabe shi ba.