Gwamna Buni ya jinjina wa Kwalejin El-Kanemi kan ɗawainiyar marayu

Gwamna Mai Mala Buni, ya yi jinjina ga kwalejin ilimin addinin Islama ta El-Kanemi da ke Maiduguri bisa jajircewarta wajen tallafa wa marayu daga Jihar Yobe.  A ziyarar da Gwamnan ya kai wa Kwalejin, wanda mataimakinsa, Idi Barde Gubana ya wakilta, ya tattauna da marayu 55 da ke karatu a ƙarƙashin gidauniyar marayu ta Abdullateef […]

Gwamna Buni ya jinjina wa Kwalejin El-Kanemi kan ɗawainiyar marayu

Gwamna Mai Mala Buni, ya yi jinjina ga kwalejin ilimin addinin Islama ta El-Kanemi da ke Maiduguri bisa jajircewarta wajen tallafa wa marayu daga Jihar Yobe. 

A ziyarar da Gwamnan ya kai wa Kwalejin, wanda mataimakinsa, Idi Barde Gubana ya wakilta, ya tattauna da marayu 55 da ke karatu a ƙarƙashin gidauniyar marayu ta Abdullateef Zabadenee.

Gwamnan ya yaba da shirin bayar da ilimi kyauta na kwalejin, inda ya kuma buƙaci ɗaliban da su kasance jakadu nagari a jihar Yobe, kuma su ci gaba da jajircewa a karatunsu.

Ya kuma yi alƙawarin tallafawa da haɗa kai da kwalejin wajen ɗaukar nauyin marayu, inda ya jaddada muhimmancin irin waɗannan ayyuka a Musulunci.

Gwamnan ya ba da gudummawar Naira miliyan 5 da kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, taliya da kuma sauran kayayyaki.

Haka kuma, su ma sauran jiga-jigan da suka raka mataimakin gwamnan sun bayar da jimillar naira miliyan 8 a matsayin tasu gudunmawar.

Daraktan kwalejin Alqadi Zubair Muhammad Wasagu, ya gode wa gwamnan bisa wannan ziyara, yana mai bayyana irin nasarorin da gidauniyar ta samu da suka haɗa da haddar kur’ani da ɗalibai 22 suka yi da kuma haddar hadisai 3,751 da ɗalibai 12 suka yi.

Gwamnatin Buni ta ba da fifiko kan ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da tsare-tsare da suka haɗa da samar da cikakkiyar hanyar sadarwa da gina asibitoci da kuma gyara makarantu a jihar ta Yobe.