Gwamna Buni ya lashe Zaben Gwamnan Yobe

Sakamakon zaben gwamna da Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Jihar Yobe ta shelanta cewar,  Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar Yobe da Rinjayen Kuri’u masu yawan gaske a tsakanin sa da abokan takarar sa.  Kwamishinan Hukumar ta zabe mai zaman kanta […]

Gwamna Buni ya lashe Zaben Gwamnan Yobe

Gwamna Mai Mala Buni

Sakamakon zaben gwamna da Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Jihar Yobe ta shelanta cewar,  Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar Yobe da Rinjayen Kuri’u masu yawan gaske a tsakanin sa da abokan takarar sa. 

Kwamishinan Hukumar ta zabe mai zaman kanta ta kasa  INEC na jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon zaben dake Damaturu, a daren nan na ranar Lahadi 19/04/2023.

Kwamishinan hukumar zaben ya  ce Gwamna Buni na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 317,113, fiye da na abokin takararsa daga jam’iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi, mai adadin kuri’u 104,259, wanda hakan na nuna gwamna Buni a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 18/04/2023.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu