Gwamna Buni ya yaba da yadda mutane suka fito zabe

INEC ta yi bajinta yadda na’urar BVAS ba ta kawo wata tangarda ba.

Gwamna Buni ya yaba da yadda mutane suka fito zabe

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya yaba bisa ga yadda jama’a suka fito don kada kuri’un su a kan lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Buni ya bayyana hakan ne jim kadan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba ta 004 da ke mazabar Bulturam /Yarimari ta garin Buni Gari a Karamar Hukumar Gujba.

A cewar Gwamna Buni, bisa ga yadda ya ga mutane sun fito don kada kuri’unsu a farar safiya fiye da yadda suka yi zaben Shugaban Kasa da ya gabata abin a yaba ne matuka.

Ya kuma yaba wa Hukumar Zabe ta Kasa INEC bisa ga yadda ta yi cikakken shiri wajen gudanar da wannan zabe musamman yadda na’urar tantance masu zabe ta BVAS ta yi aikin ta ba tare da samun wata tangarda ba.

Gwamna Buni ya yi fatan samun zabe mai inganci yadda al’umma za su aminta da shi.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54