Gwamna Buni ya yi wa fursunoni 115 afuwa

Gwamnan ya bukaci wadanda aka saki da guji sake aikata laifuka.

Gwamna Buni ya yi wa fursunoni 115 afuwa

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi wa fursunoni 115 da aka zabo daga gidajen gyaran hali afuwa a fadin jihar.

Yafewar ta biyo bayan nazari da kwamitin da aka kafa kan jin-kai karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnati kuma babban mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin shari’a, Barista Sale Samanja ya yi.

Da yake gabatar da rahoton, Samanja ya ce afuwar da gwamnan ya yi, ya yi daidai da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima da ya ba shi dama.

Barista Samanja ya ce duk wadanda aka saki sun yi farin ciki da wannan karamci da gwamnan ya yi musu, sun kuma yi alkawarin amfani da ’yancinsu wajen gyara kura-kuran da suka yi a baya.

Da yake karbar rahoton kwamatin a gidan gwamnati da ke Damaturu, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana rahoton afuwar ga fursunonin a matsayin muhimmin abu da gwamnatinsa ke yi na rage cunkoso a gidajen gyaran hali.

Buni ya ce a matsayinsa na gwamna, ya yi imani da matakan da za su saukaka gyaran fursunoni.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wajen rage yawan fursunoni a gidan yari.

Gwamnan ya bayyana fatan cewa wadanda aka saki sun koyi darasi kuma za su kaucewa maimaita abin da ya kai su gidan yari.

Ya yaba wa kwamitin bisa kokarin da suka yi wanda ya kai ga samun nasarar tantance fursunonin 115 da aka yi musu afuwa.

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno