Gwamna Dakingari ya gabatar wa Majalisar Kebbi kasafin Naira biliyan 131
Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya mika wa Majalisar Jihar kasafin Naira biliyan 131 da miliyan 732 da dubu 791 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2014.Gwamnan ya ce daga cikin adadin kudin an ware Naira biliyan 31 da miliyan 570 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka […]
Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya mika wa Majalisar Jihar kasafin Naira biliyan 131 da miliyan 732 da dubu 791 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2014.
Gwamnan ya ce daga cikin adadin kudin an ware Naira biliyan 31 da miliyan 570 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware Naira biliyan 100 da miliyan 162 don gudanar da manyan ayyuka.
Da yake gabatar da kasafin kudin a gaban Majalisar Dokokin Jihar, Gwamna Sa’idu dakingari, ya ce an tsara kasafin kudin ne domin ya zama daidai da kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin kasashen duniya da kuma nan cikin gida.
Gwamnan ya ce kasafin kudin ya kunshi bukatar bunkasa samar da ayyukan yi da samar da abinci da kuma inganta yanayin rayuwar jama’a da fatan samun kyakkywan ci gaban jihar.
A kasafin na badi, sashin tattalin ariziki wanda ya kunshi aikin gona da kiwon dabbobi da samar da wutar lantarki da sufuri yana da Naira biliyan 50 da miliyan 840. Sai bangaren bunkasa rayyuwar jama’a wanda ya kunshi ilimi da kiwon lafiya da watsa labarai da kimiya da kare-kere ya tashi da Naira biliyan 24 da miliyan 500.
bangaren mulki ya tashi da Naira 17 da miliyan 800, sashIn sufuri ya samu kason Naira biliyan 41 da miliyan 219.
Da yake amsar kasafin kudin shugaban majalisar, Alhaji Aminu Musa Habib Jega, ya yi alkawarin cewa majalisa za ta yi nazarin kasafin kudin da kuma amincewa da shi cikin gaggawa ta yadda za a fara aiwatar da shi ba tare da jinkiri ba domin amfanin al’ummar jihar.