Gwamna dakingari ya koka kan halin jami’an Kwastam

Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya ce ko jami’an Kwastam sun so ko ba su so ba, sai an shigo da kayayyakin more rayuwa a jihar.Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Nasamu Gaskiya Youth Forum (NAGAYOFO) daga kananan hukumomi jihar 21 suka kai masa ziyarar ban girma da […]

Gwamna dakingari ya koka kan halin jami’an Kwastam
Gwamna dakingari ya koka kan halin jami’an Kwastam

Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya ce ko jami’an Kwastam sun so ko ba su so ba, sai an shigo da kayayyakin more rayuwa a jihar.
Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Nasamu Gaskiya Youth Forum (NAGAYOFO) daga kananan hukumomi jihar 21 suka kai masa ziyarar ban girma da mika kokon bararsu na ya taimaka wa kungiyar.
Alhaji Sa’idu dakingari ya ce hanyoyin da gwamnatinsa ta giggina wa mazauna karkara a ko’ina a cikin jihar har zuwa iyaka da kasashen Nijar da Benin, za su sanya ba jihar a damar safarar kayayyakin more rayuwa ga al’ummar jihar Kebbi koda jami’an Kwastam ba su so ba.
Gwamnan ya shaida wa ’ya’yan kungiyar cewa su ci gaba da hada kai a tsakaninsu, kuma mambobinta su rika biyayya ga shugabanninta, inda ya ce ta haka ne za su samu ci gaba mai ma’ana.
Kuma ya bukaci su rika lura da bakin ido da ba su yarda da su ba, don su kai rahoto ga ’yan sanda mafi kusa da su.
A jawabin shugaban kungiyar Alhaji Bashir Yariman Mera, ya shaida wa Gwamnan cewar dukkan kungiyoyin da aka kirkiro a jihar a 1999 duk sun mutu amma ban da kungiyarsu ta Nasamu Gaskiya Youth Forum (NAGAYOFO), saboda shugabannin kungiyar sun jajirce kan tafiyar da harkokinta ta hannyar kulla-kula taro sisi domin cimma burinsu na hada kan matasa da kuma wayar musu da kai kan illar zaman banza da kauce wa bangar siyasa ko bin gidajen masu kudi suna maula.