Gwamna El-Rufa’i ya rage kwamishinoninsa zuwa 13

Ranar Talatar da ta gabata ne Gwam-nan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bada sanarwar rage yawan kwamishinoninsa daga 24 zuwa 13 da zai yi aiki da su a jihar kuma ta hade ma’aikatunta 19 sun koma 13. Gwamna El-Rufa’i ya ce hakan zai rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen tafiyar da al’amuranta.Gwamnan […]

Gwamna El-Rufa’i ya rage kwamishinoninsa zuwa 13
Gwamna El-Rufa’i ya rage kwamishinoninsa zuwa 13

Ranar Talatar da ta gabata ne Gwam-nan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bada sanarwar rage yawan kwamishinoninsa daga 24 zuwa 13 da zai yi aiki da su a jihar kuma ta hade ma’aikatunta 19 sun koma 13.

Gwamna El-Rufa’i ya ce hakan zai rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen tafiyar da al’amuranta.
Gwamnan ya kuma rage yawan mataimaka da kwamishinonin da zai dauka domin taimaka masa shi da Mataimakinsa wajen gudanar da aikinsu.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Samuel Aruwan ce ta bayyana haka, inda sanarwar ta ce, “Idan za a tuna a kwanakin baya Gwamna ya sha nanata kudirin gwamnatinsa na samar da abubuwan more rayuwa ga jama’a ta hanyar rage dimbin kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.”
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta bambamta da sauran gwamnatoci masu daukar daruruwan mashawarta.
Sannan ya ce Ma’aikatar Filaye da Safiyo za ta zauna a karkashin ofishin Gwamna yayin da Ma’aikatar Bunkasa Karkara za ta zauna a karkashin ofishin Mataimakin Gwamnan Mista Barnabas Bala Banted.