Gwamna El’rufai ya sa dansa a makarantar Gwamnati
A yau Litinin Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad Elrufai ya cika alkawarin da ya dauka shekarun baya na cewa, zai saka dansa Abubakar Saddique El-Rufai a makarantar gwamnati. Gwamnan tare da uwar yaron Ummi El-Rufai sun kai Abubakar dan shekara shida Makaranta Kaduna Capital School da ke a Malali Kaduna inda aka yi masa rajista. […]
A yau Litinin Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad Elrufai ya cika alkawarin da ya dauka shekarun baya na cewa, zai saka dansa Abubakar Saddique El-Rufai a makarantar gwamnati.
Gwamnan tare da uwar yaron Ummi El-Rufai sun kai Abubakar dan shekara shida Makaranta Kaduna Capital School da ke a Malali Kaduna inda aka yi masa rajista.
Shugaban makaranta Ibrahim Yunusa, ya tabbatarwa da Aminiya cewa an yi wa yaron rajista a makarantar.
“Eh yau Litinin da safe gwamna El-Rufai da matarsa watau uwar yaron sun zo makarantar nan inda suka yi wa dansu Abubakar Siddique El-Rufai rajista aji daya. Na kuma yi murna da karbar dan nasa domin hakan zai taimaka wajen inganta makarantun gwamnati.

“Gwamnan ya kuma bayyana min cewa, ya zo ne a matsayina na uba kamar kowa sannan kuma ya cika alkawarinsa ne ga jama’a,” in ji shi.
Shugaban Makarantar ya kuma ja hankalin sauran masu rike da mukaman gwamnati da su yi koyi da Gwamnan domin yin hakan ne zai taimaka wajen maido da martabar makarantun gwamnati.
An dai kafa makarantar Kaduna Capital School ne a shekarar 1957 kuma makarantar gwamnati ce.
