Gwamna Fashola ya bukaci a kirkiro ’yan sandan jiha

Tabarbarewar harkokin tsaron da Najeriya ke fama da shi  yasa  bukatar  samar da ’yan sandar jiha ta zama  wajibi,  domin tallafa wa tsaro a cikin kasa, idan ba haka ko lamarin ya ci gaba da sukurkucewa, a cewar Gwamnan jihar Legas  Mista Babatunde  Raji Fashola.Gwamnan ya yi wannan kalamin ne a karshen taron ’yan majilisar […]

Gwamna Fashola ya bukaci a kirkiro ’yan sandan jiha
Gwamna Fashola ya bukaci a kirkiro ’yan sandan jiha

Tabarbarewar harkokin tsaron da Najeriya ke fama da shi  yasa  bukatar  samar da ’yan sandar jiha ta zama  wajibi,  domin tallafa wa tsaro a cikin kasa, idan ba haka ko lamarin ya ci gaba da sukurkucewa, a cewar Gwamnan jihar Legas  Mista Babatunde  Raji Fashola.
Gwamnan ya yi wannan kalamin ne a karshen taron ’yan majilisar dokokin jihars da suka yi da bangaren zartaswa  na jihar, domin musayar  ra’ayi  game da yadda  za su  ci gaba da  tafiyar  da  ayyukan su ba  tare  da fuskantar  matsala ba.  Kuma  sun kara  fahimtar  juna  ta  sanin ina suka  fito, ina  suka  dosa.
Ya ce idan dai  zai iya tuna  abin da dokar  kasa  ta ce  game da samar da ’yan sanda, yasan  cewa ba inda aka yi hani da  samar da  ’yan sandar jiha. Domin a cewarsa, sai  an samu hadin gwiwa ne tsakanin masu gudanar da mulki sa’ilin ne za a samu  sauki  a kome  aka kudiri  aniyar  gudanarwa.
 Gwamnan ya yi  kira ga majalisun kasar  nan guda biyu, da su  sake duba  wannan batu  da idon basira, kuma su  fitar da  son rai ciki, domin samar da dokar kasa  da  za ta bada  damar  kirkiro da ’yan sandan jiha, wanda  ya ce  zai taimaka  matuka  gaya  wajen tsaron.
Shi kuwa mai baiwa gwamna  shawara a harkokin majilisa, Folami Muslim Oloruntele, cewa ya yi,  makasudin wannan taron, shi ne,  a yi musayar  ra’ayi  tsakanin bangaren mulki  da  masu yin dokoki, ta  yadda  zai amfani jama’ar  jihar da ma kasa  baki  daya.