Gwamna Gaidam ya ba zakarun musabaka kyautar motoci
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ba da kyautar motoci biyu a madadin gwamnatin jihar ga Hafiz kasimu Muhammad da Malama A’isha Abdulmutallib da suka zamo zakarun gasar karatun Alkur’ani na jihar karo na 23 a bangaren maza da mata.Gasar wadda aka gudanar a Masallacin Juma’a na Cibiyar Kula da Addinin Musulunci da ke […]

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ba da kyautar motoci biyu a madadin gwamnatin jihar ga Hafiz kasimu Muhammad da Malama A’isha Abdulmutallib da suka zamo zakarun gasar karatun Alkur’ani na jihar karo na 23 a bangaren maza da mata.
Gasar wadda aka gudanar a Masallacin Juma’a na Cibiyar Kula da Addinin Musulunci da ke Damaturu ta samu halartar manyan jami’an gwamnatin jihar da Mai martaba Sarkin Damaturu Shehu Hashimi Ibn El-Kanemi da kuma malaman addinin Musulunci.
Da yake jawabi a wurin rufe gasar Gwamna Gaidam ya ce saboda a karfafa wa matasa gwiwar shiga gasar ce gwamnati ke shirya gasar da ba da kyauta mai tsoka ga wadanda suka yi fice a gasar.
Ya ce baya ga motoci ga zakarun gasar gwamnati ta kebe Naira dubu 500 ga wadanda
suka zo na biyu da na uku a kowane bangare da kuma wasu kananan kyaututtuka irin su kekunan hawa da na dinki da sauransu ga sauran wadanda suka tagaza a gasar.
Gwamnan ya gargadi matasa Musulmi su guji yawaita karanta littattafan tatsuniyoyi da almara da ke koyar da dabi’un da suka yi hannun riga da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), maimakon haka su juya ga karatun Alkur’ani Mai girma don tsira duniya da kiyama.
Sai yakirayi zakarun gasar su kara kaimi domin yi wa jihar kyakyyawa wakilci a gasar a kasa zuwa a duniya.
Ya kuma nada zakaran gasar Malam kasimu Muhammad a matsayin babban magatakardar babbar kotun jihar.