Gwamna Gaidam ya gamsu da aikin Kwamitin Hajji na Jihar

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yaba da irin nasarorin da Kwamitin Aikin Hajji na Jihar ya samu a bara a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Bade Alhaji Abubakar Umar Sulaiman. Gwamna Gaidam ya bayyana a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu a ranar Talatar da ta […]

Gwamna Gaidam ya gamsu da aikin Kwamitin Hajji na Jihar
Gwamna Gaidam ya gamsu da aikin Kwamitin Hajji na Jihar

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yaba da irin nasarorin da Kwamitin Aikin Hajji na Jihar ya samu a bara a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Bade Alhaji Abubakar Umar Sulaiman.

Gwamna Gaidam ya bayyana a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce kwamitin nuna kokari wajen gudanar da ayyukansa a nan Najeriya da kuma kasar Saudiyya.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta ji dadi dangane da wannan namijin kokari da kwamitin Amirul Hajjin da sauran membobinsa bisa tsayin daka da jajircewarsu wajen samun wannan nasara.
Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatin Jihar Jigawa dangane da hadin kan da ta bai wa ma’aikatan Hukumar Alhazai ta Jihar a lokacin jigilar maniyyatan jihar daga filin jirgin saman Dutse zuwa kasa Mai tsarki.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya ba da tabbaci ga kwamitin cewa gwamnati za ta yi aiki da shawarwarin kwamitin domin shirya aikin Hajji mai zuwa a kan lokaci.
Da yake maida jawabi Amirul Hajjin kuma Sarkin Bade Alhaji Abubakar Sulaiman ya ce Mutum 2,261 ne suka sauke farali a aikin Hajjin bara kuma cikin taimakon Allah sun gama wannan aikin ibada lafiya ba tare da wata babbara matsala ba. Ya ce in ban da wasu kananan matsaloli da suka fuskanta da suke da alaka da matsalar tsaro da ta zama alakakai a yankin kuma duk mahajjatansu sun dawo gida lafiya.
Alhaji Abubakar Umar Sulaiman ya ce nasarorin da kwamitin ya samu sun ta’allaka ne da irin hobbasar da gwamnatin jihar ta yi wajen kyautata tsarin aikin da saukake wa mahajjatan wasu dawainiyoyi tun daga nan gida har zuwa Saudiyya da suka hada da abinci da ihrami da wurin kwana da motocin da suka rika jigilarsu a can Saudiyya.