Gwamna Inuwa ya buƙaci haɗin kai da juriya a sabuwar shekara

Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar ƙudirinsa na ci gaba da samar musu da ababen more rayuwa.

Gwamna Inuwa ya buƙaci haɗin kai da juriya a sabuwar shekara

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da Najeriya baki ɗaya da su haɗa kai da juriya wajen aiki tare don samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

A saƙonsa na Sabuwar Shekara, Gwamnan ya buƙaci al’umma su yi tunani kan darussan shekarar da ta gabata tare da shiga sabuwar shekara da yaƙini mai kyau.

“Shekarar 2025 tana cike da alƙawura masu kyau gare mu baki ɗaya. Mu dage wajen sadaukarwa ga zaman lafiya, ci gaba, da walwala,” in ji shi.

Gwamnan, ta hannun Babban Daraktan Harkokin Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli, ya yaba da juriyar al’ummar Gombe wajen fuskantar matsalolin tattalin arziƙi a baya-bayan nan.

Ya jaddada cewa haɗin kai da juriya su ne mabuɗin nasarar duk wata matsala.

Ya kuma lissafo nasarorin gwamnatinsa, ciki har da biyan mafi ƙarancin albashi, biyan bashin fansho, da sanya hannu kan dokar kare haƙƙoƙin nakasassu.

Gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa wajen ci gaban masana’antu, gine-gine, da samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci.

“Mun kafa tubali mai girma don ci gaba. Tare da goyon bayanku, za mu cimma burikanmu baki ɗaya,” in ji Gwamna Inuwa.

Har wa yau, ya gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa, inda ya buƙaci su ci gaba da haɗa kai don gina makoma mai kyau a Jihar Gombe.