Gwamna Kano ya karɓi rahoton kwamitin mafi ƙarancin albashi
Gwamnan ya jaddada aniyarsa ta kyautata wa ma’aikatan jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin ma’aikatan jihar, bayan ya karɓi rahoton da kwamitin mafi ƙarancin albashi ya gabatar.
Kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana a ranar Talata.
Ya bayyana cewa kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Usman Bala, an ba shi aikin nazari da bayar da shawara kan tsarin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar.
Yayin gabatar da rahoton, Gwamna Abba ya yaba wa kwamitin kan aiki da shawarwarin da suka gabatar masa.
Ya ce shawarwarin da suka bayar za su taimaka wa gwamnati wajen tsara manufofi masu ɗorewa.
“Mun zaɓi wannan kwamitin saboda muna da tabbacin za su kawo shawarwari masu amfani da sabbin dabaru,” in ji gwamnan.
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa ma’aikata cewa gwamnatinsa tana da ƙudirin cika alƙawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Ya yi kira gare su da su ƙara haƙuri, yayin da gwamnatin ke nazarin shawarwarin da kwamitin don tabbatar da suna kan doka.
Ya bayyana cewa zai sanar da matakin da ya ɗauka game da rahoton ya gabatar masa a mako mai zuwa.
Shugaban kwamitin, Usman Bala, ya ce sun gabatar da shawarwarin bisa la’akari da yanayin tattalin arziƙin da Kano ke ciki a yanzu.
Ya bayyana tabbacin cewa tsarin albashin da aka bayar zai kasance mai ɗorewa kuma zai inganta yanayin ma’aikatan gwamnati.