Gwamna Lalong ka yi hattara da masu neman a cire Jos daga zaben Filato – Iliyasu
Wani dan kasuwa kuma shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta Jihar Filato, Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi kira ga gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong kan ya yi hattara da wadanda suke kokarin ganin cewa an fitar da karamar hukumar Jos ta Arewa daga zaben kananan hukumomin jihar, da za a gudanar a watan biyu […]

Wani dan kasuwa kuma shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta Jihar Filato, Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi kira ga gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong kan ya yi hattara da wadanda suke kokarin ganin cewa an fitar da karamar hukumar Jos ta Arewa daga zaben kananan hukumomin jihar, da za a gudanar a watan biyu na shekara mai zuwa.
Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce wannan kokari da wasu suke yi, ba damakoradiyya ce ta gaskiya ba, saboda an dade ba ayi zabe ba a karamar hukumar Jos ta Arewa. Wanda yin hakan kawo wa jihar Filato ci baya ne kwarai da gaske. Ya ce ya kamata a cikawa al’ummar karamar hukumar Jos alkawarin da aka yi masu, na cewa za a gudanar masu da zaben shugabannin wannan karamar hukuma.
Haka kuma ya yi kira ga al’ummar karamar hukuma ta Jos ta Arewa su hada kai su cigaba da zaman lafiyar da aka samu a wannan karamar hukuma. Su manta da bambancin addini da kabila su zabi mutumin da ya cancanta wanda zai kawo masu cigaba a karamar hukumar a wannan zabe da za a gudanar.
Daga nan ya yabawa gwamnatin Jihar ta Filato kan wannan yunkuri da ta ke yi, na gudanar da zaben kananan hukumomin jihar. Ya ce wannan abu ne mai kyau wanda aka dade ana jira, domin zaben kananan hukumomi zabe ne da yake amfanar talaka kai tsaye, saboda kusancin shugabannin kananan hukumomi da talakawansu.