Gwamna Lalong ya ba Sakataren ‘Yan Agajin Izala Kwamishina
Sakataren ’Yan Agaji na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah W Ikamatis Sunnah ta Kasa Malam Muhammad Muhammad Abubakar yana daya daga cikin sunayen sababbin kwamishinoni 23 da Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya mika ga Majalisar Dokokin Jihar Filato domin tantancewa. Sunayen sababbin kwamishinonin ya nuna cewa akwai tsofaffin kwamishinoni 11 da aka sake dawo […]
Malam Muhammad Muhammad Abubakar
Sakataren ’Yan Agaji na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah W Ikamatis Sunnah ta Kasa Malam Muhammad Muhammad Abubakar yana daya daga cikin sunayen sababbin kwamishinoni 23 da Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya mika ga Majalisar Dokokin Jihar Filato domin tantancewa.
Sunayen sababbin kwamishinonin ya nuna cewa akwai tsofaffin kwamishinoni 11 da aka sake dawo da su sannan aka kawo sababbin kwamishinonin 12.
Da yake karanta wa ’yan Majalisar Dokokin sunayen sababbin kwamishinonin a ranar Talatar da ta gabata, Shugaban Majalisar Honarabul Ayuba Abok ya ce sunayen tsofaffin kwamishinonin 11 da aka sake dawo da su sun hada da Alhaji Dayyabu Garga da Yakubu Dati da Mista Dan Manjang da Idi Usman Bamayi da Bictor Lapang da Regina Soemlat da Tamwakat Weli da Sylbester Wallangko da Elizabeth Wapmuk da Dakur Jude Eli da kuma Pam Botmang.
Sababbin kwamishinonin 12 da aka gabatar sun hada da Chrisantus Ahmadu da Muhammad Muhammad Abubakar da Jerry Werr da Sambo Rebecca Adar da Abe Aku da Dung Musa Gyang da Tapgun Sylbanus da Nimkong Lar-Ndam da Kak Mena Goteng Audu da Ibrahim Sa’ad Bello da Rimben Bitrus Zulfa da kuma Hosea Istifanus Finangwai.
Majalisar ta sanya ranar 23 ga wannan wata a matsayin ranar da za ta fara tantance sunayen kwamishinonin.