Gwamna Lalong ya bukaci Fulani da Berom su maida wukarsu kube
Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong ya bukaci al’ummar Fulani da Berom su mayar da wukarsu kube ta hanyar kawo karshen kashe-kashen da suke yi wa juna, kuma su rika hakurin zama da junansu. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Nasiru Oki da shugabannin kungiyar […]
Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong ya bukaci al’ummar Fulani da Berom su mayar da wukarsu kube ta hanyar kawo karshen kashe-kashen da suke yi wa juna, kuma su rika hakurin zama da junansu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Nasiru Oki da shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders na kananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu da Barikin Ladi a gidan saukar baki na gwamnatin jihar da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata.
Mai taimaka wa Gwamnan a bangaren watsa labarai Mista Emmanuel Nanle ya shaida wa manema labarai cewa, an shirya ganarwa ce saboda hare-haren baya-bayan nan da bangarorin biyu suke kai wa juna.
Mista Nanle ya ce a lokacin ganawar Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kashe-kashe a tsakanin kabilun ya ki ci ya ki cinyewa, kuma ya bukaci su rungumi zaman lafiya.
“Gwamna ya bukaci bangarorin su mayar da wukakensu cikin kube, kuma su rungumi zaman lafiya don a samu ci gaba a jihar. Ya kuma bukaci su rika hakuri da juna don a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar,” inji Nanle.
Ya ce nan gaba Gwamnan zai yi irin wannan zama da shugabannin kabilar Berom kamar yadda ya yi da na Fulani don a yi wa tufkar rikicin da ke tsakanin kibilun hanci.
“Shugabannin Fulani sun gabatar da korafe-korafensu a gaban Gwamna, inda ya tabbatar musu za a duba su, sannan a samo hanyar tabbatar da zaman lafiya.” inji shi.
Ya ce Gwamna ya kuma umarci jami’an tsaro su samo sababbin dabaru don magance rikicin da ke tsakanin kabilun biyu.