Gwamna Lalong ya sassauta dokar hana fita a Jos
Sassaucin da aka yi wa dokar zai fara aiki ne daga ranar Alhamis.
Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato, ya sassauta dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 da ya kakaba a Karamar Hukumar Jos ta Arewa biyo bayan kisan matafiya da aka yi a kan hanyar Rukubu da ke wajen garin Jos a ranar Asabar.
Matakin hakan ya biyo bayan zaman Majalisar Tsaron Jihar da aka gudanar ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Jos, babban birnin Filato, inda gwamnan ya saurari bayanai daga Shugabannin Hukumomi Tsaro sannan ya yi nazari kan halin da ake ciki.
- Najeriya da Saudiyya sun kulla yarjejeniyar yakar safarar migayun kwayoyi
- ‘Yan bindiga sun sace daliban Islamiyya a Katsina
Karkashin wannan sassauci da gwamnan ya yi wa dokar hana fitar, a yanzu an umurci jama’a da su takaice zirga-zirgarsu daga karfe 6.00 na safe zuwa 6.00 na yammaci.
Sanarwar da Darektan Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Filato, Dokta Makut Simon Machum ya raba wa manema labarai a yammacin Laraba, ta ce sassaucin da aka yi wa dokar zai fara aiki ne daga ranar Alhamis, 19 ga watan Agustan 2021.
A cewarsa, dokar ta hada da Kananan Hukumomin Bassa da Jos ta Kudu wanda a baya suma aka kakaba musu dokar takaita zirga-zirga saboda fargabar abin da ka iya biyo bayan kisan matafiyan da ake zargi matasan kabilar Irigwe suka yi.