Gwamna Lalong zai binciki Jang kan yadda ya sayo motocin da ya raba bashi

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa kwamitin da zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin jihar a karkashin Jonah Jang ta sayo kananan motoci da kekuna masu kafa da ta raba bashi a lokacin mulkinta.Da yake kaddamar da kwamitin, Gwamna Simon Lalong ya ce sun kafa kwamitin ne domin ya binciko yadda gwamnatin da ta […]

Gwamna Lalong zai binciki Jang kan yadda ya sayo motocin da ya raba bashi
Gwamna Lalong zai binciki Jang kan yadda ya sayo motocin da ya raba bashi

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa kwamitin da zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin jihar a karkashin Jonah Jang ta sayo kananan motoci da kekuna masu kafa da ta raba bashi a lokacin mulkinta.
Da yake kaddamar da kwamitin, Gwamna Simon Lalong ya ce sun kafa kwamitin ne domin ya binciko yadda gwamnatin da ta gabata, ta sayo kananan motoci da Babura masu kafa uku ta raba bashi ta hanyar shirin yaki da talauci.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Rufus Bature ya ce kuna sane da cewa Gwamnatin Tarayya ta kirkiro tsare-tsaren yaki da talauci ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa da ciyar da ’yan makaranta da bayar da basussuka ga mata da matasa ta ofishin Mataimakin Shugaban kasa domin taimaka wa al’ummar kasar nan. “Don haka ya zama wajibi gwamnatin jihar ta tantance irin wannan tallafi da ake samu daga Gwamnatin Tarayya, domin mu hada hannu wajen yakar tallauci a jihar nan, don haka muka kafa kwamitin domin ya gano yadda aka sayo motoci da babura masu kafa uku da yadda aka raba su,” inji shi.
Kwamiti da ke karkashin shugabancin Mista Morris Dashe da Aliyu Baba Tirmiziyu a matsayin sakatare, yana da wakilan da suka hada da Injiniya John S. Daya da Mista Edward Yakwai da Mista Yusuf Izam da Barista Joel Tahban da kuma Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda G.A.Grimah.
Ayyukan da aka bai wa kwamitin su ne gano yawan motoci da Babura masu kafa uku da gwamnatin Jang ta sayo da gano yadda aka raba su da sunayen wadanda aka rabawa da adireshinsu da yawan kudin da suka biya da kudin da ake bin su bashi da kuma karbo sauran kudin da ake bi bashi, kuma ya mika rahotonsa cikin wata biyu.