Gwamna Lamido ka tallafa wa kungiyoyin al’umma
A halin da kasar nan ta tsinci kanta na matsalar tattalin arziki da zamantakewa, musamman kan al’amuran da suka shafin tsaron rayuka da dukiyar al’umma, ya zama dole a matsayinmu na ’ya’yan jihar Jigawa, mu bai wa Gwamnanmu alhaji Sule Lamido shawara kan yadda zai tallafa wa kungiyoyi, don ci gaban al’ummar jiharmu da kasa […]
A halin da kasar nan ta tsinci kanta na matsalar tattalin arziki da zamantakewa, musamman kan al’amuran da suka shafin tsaron rayuka da dukiyar al’umma, ya zama dole a matsayinmu na ’ya’yan jihar Jigawa, mu bai wa Gwamnanmu alhaji Sule Lamido shawara kan yadda zai tallafa wa kungiyoyi, don ci gaban al’ummar jiharmu da kasa baki daya. ’yan Jigawa da ke zaune a wasu jihohin ksar nan na da gudunmuwar da za su bayar wajen inganta rayuwar rayuwar al’umma, musamman in an yi la’akari da yadda ’yan Najeriya da ke zaune a wasu kasashen duniya ke ta fafutikar ganin an ba su damar shiga a dama da su a harkokin kasar nan, har ma ta kai ga suna son lallai sai sun kada kuri’unsu a zaben 2015.
Sanin kowa ne, kuniyoyin zabi sonka da sauran kungiyoyi wadanda ba ruwansu da gwamnati (NGOs) sun taimaka matuka wajen ayyukan gayya da tsaftar muhalli, al’amarin da a halin yanzu an yi watsi da shi, ko kuma in ce an dan ja da baya. Sannan a da ko bakon wanzami ya sauka a gari, tilas sai mai unguwa ya san da zamansa, har ma in zo da alkhairi ko a akasinsa, a sanar da hukuma, ta yadda za ta dauki matakin da ya dace a kansa. Don haka a da ba a cika samun matsalolin zamantakewa da fadace-fadacen siyasa irin na yanzu ba. Kuma mutane ba za su rika yin tafiyar ci-rani a garuruwan da ba nasu ba, matukar suna da abubuwan yi.
Da yake Hausawa na cewa, ‘Tafiya mabudin ilimi,” kuma Marigayi Alhaji Dokta Mamman Shata Katsina, ya taba yin wakar “Yawon duniya mafarki ne Alhaji Shata.” Ina ganin duk wanda ya tafi yawon duniya, ko fatauci ko neman ilimi a wani gari ko kasar da ba tasa ta haihuwa ba, ya neman sani ko samo harkokin inganta rayuwa don ya kawo su garinsu, al’ummar da ba su amu damar yin tafiya irin tasa ba su karu. Idan kuwa ya koyo miyagun dabi’u, ba a Ankara ba, ya zo ya yada su a tsakanin al’umma, to sai mu ce mun shiga uku mun lalace. karamin takadiri dai shi ne cutar Ebola da akwanan nan ta shigo Najeriya, alhali tun farko a kasashen Saliyo da Gini da Laberiya muka rika jinta, amma da aka yi sakaci matafiya suka shigo mana da ita, ko mutum bai kamu ba, to yana cikin dar-dar, musamman yadda ak yi ta kwakwazo a kan illarta a daukacin fadin duniya.
Bisa la’akari da al’amuran da ke faruwa a kasrmu Najeriya, lallai na ga ya zama wajibi in roki Gwamnanmu Alhaji Dokta Sule Lamido kan ya himmatu wajen tallafa wa kungiyoyin al’umma da ke fafutikar kare muhalli da hakkokin al’umma da gyaran zamantakewa da siyasa da bunkasa tattalin arziki. Musamman ma mu ’yan Jihar Jigawa da ke zaune a Babban Birnin Tarayya Abuja, mun kafa kungiyar ’yan masarautar Gumel, mun kuma samu gagarumar nasarar fadakarwa da wayar da kan al’umma, kan yadda za su tafiyar da harkokin kasuwancinsu da sana’o’I da hakuri wajen zama da dimbin al’umma da suka sha bamban da su, ta fuskar al’adu da addini. Irin wannan manufa tamu, muna kyautata zaton za ta haifar da zaman lafiya a Najeriya. Don haka muke fata Gwamna Sule Lamido zai agaza wa kungiyoyin ’ya’yan jihar Jigawa, wajen ba su duk talafin da ya dace, ta yadda za su yi tasiri wajen gyaran muhalli da sauran al’amuran da suka shafi jama’a. Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga daukacin ’ya’yan Jihar Jigawa da su kafa kwakkwarar kungiya, ba tare da nuna bambancin masarauta ba, ko yare ko kabila.
Lallai mu san kanmu, mu fahimci wadanda muke mu’amala ta yau da kullum tare das u. Uwa-uba, mu roki Allah Ya shige mana gaba a daukacin al’amuranmu. Malamai dai sun yi bayani cewa, samun nasarar addu’a a wurin Allah yana da nasaba da kyakkyawar niya da yakini, tare da aiki tukuru, don cimma buri, a rayuwar duniya da ta lahira. Saboda haka mu kasance masu nufi na gaskiya, mu sauke nauyin d aya rataya kanmu, sannan mu tursasa shugabanni su ma su sauke nasu.
Idan muka yi wa kwunanmu garambawul, kuma muka samu tallafi da goyon baya daga shugabanninmu, musamman Gwamna da wakilai a majalisar kasa, to ba mu da wata hujja za mu rika jiran cewa komai sai gwamnati ta yi mana. Kowane dan Adam ya tabbatar cewa yana da irin gudunmuwar da zai bai wa al’umma, kafin ma ya tambayi al’ummar wata gudunmuwa, musamman idan mutum baligi ne, kuma akili (Balagaggen mai hankali).
Maigyale ya rubuto makalarsa ne daga Masaka, Jihar Nasarawa 08030630164