‘Gwamna Lamido ya jawo faduwar PDP a Jigawa’

daya daga cikin shugabannin matasan Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa, Malam Zakar Ali Zaki wanda ake yi wa lakabi da Rediyo ya danganta faduwar jam’iyyarsu a zabubbukan da suka gabata a jihar a kan Gwamna Sule Lamido. Malam Zakar ya bayyana haka ne a tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce, Gwamna Lamido […]

‘Gwamna Lamido ya jawo faduwar PDP a Jigawa’
‘Gwamna Lamido ya jawo faduwar PDP a Jigawa’

daya daga cikin shugabannin matasan Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa, Malam Zakar Ali Zaki wanda ake yi wa lakabi da Rediyo ya danganta faduwar jam’iyyarsu a zabubbukan da suka gabata a jihar a kan Gwamna Sule Lamido.

Malam Zakar ya bayyana haka ne a tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce, Gwamna Lamido mutum ne da ba ya daukar shawara sannan duk kokarin da ’yan PDP ke yi domin ci gaban jihar ba ya yaba musu.
Malam Zakar ya zargi Gwamna Lamido da kin ba ’yan jam’iyyar damar fito da ’yan takarar da jama’a ke so kuma suka fi cancanta su shugabance su. “Tsayar da Alhaji Aminu Ibrahim Ringim a matsayin dan takarar Gwamna a PDP a jihar ba laifi ba ne, amma kuskuren da aka samu shi ne Gwamna Lamido bai ba ’yan jam’iyyar da suka cancanci takara ba tun daga mukaman sanatoci da ’yan Majalisar Wakilaii da kuma na jiha domin a zabe su.