Gwamna Liyel Imoke ya dakatar da mukarabansa 20 daga aiki

Gwamnan  Jihar Kuros Riba, Sanata Liyel Imoke ya dakatar da mukarrabansa  ashirin (20) daga aiki har sai abin da hali ya yi.Dakatarwar, kamar yadda  sakataren gwamnatin jihar, Mista  Michael Aniah, ya bayyana a wata takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kalaba, ta ce gwamnan ya fusata ne sakamakon kekasa kasar da suka […]

Gwamna Liyel Imoke ya dakatar da mukarabansa 20 daga aiki

Gwamnan Jihar Kuros Ribas Liyel ImokeGwamnan  Jihar Kuros Riba, Sanata Liyel Imoke ya dakatar da mukarrabansa  ashirin (20) daga aiki har sai abin da hali ya yi.
Dakatarwar, kamar yadda  sakataren gwamnatin jihar, Mista  Michael Aniah, ya bayyana a wata takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kalaba, ta ce gwamnan ya fusata ne sakamakon kekasa kasar da suka yi su halarci bikin ranar yaki da cutar sida ta duniya da aka gudanar a fadin kasar nan da ma sauran sassa na duniya.
Sanarwar dakatarwar ta cigaba da bayyana cewa an umarci duk wanda abin ya shafa da ya mika ragamar ofishinsa ga manyan sakatarorin ofisoshinsu. Gwamnati ta nuna takaicin ganin, in banda gwamnan da wasu ’yan kalilan na mataimakansa masu ba shi kariya ta musamman, babu wani da ya halarta.
Kwamishinonin da aradun gwamnatin ta fada wa sun hada da kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Mista Attah Ochinke; kwamishinan kudi, Etim Caifas; kwamishinar kula da  harkokin mata, Misis   Edak Iwuchukwu; kwamishinar walwala da jin dadin jama’a, Misis Patricia Endeley; kwamishinan muhalli,  Dokta Sandy Onor; kwamishinan albarkatun ruwa, Elemi Etowa; kwamishinan aikin gona, James Aniyom.
bangaren masu bayar da shawarwari na musamman da fushin gwamnatin ya rutsa da su kuma sun hada da  Wilfred Usani, ma’aikatar yawon shakatawa da bude ido;  sai na bangaren harkokin addinai,  Eyo Okpo-Ene; sai  Fabian Okpa, na ma’aikatar ayyuka na musamman; sai Gerald Adah na ma’aikatar zuba jari; sai  Effiong Bassey na albarkatun kasa, sai kuma  Fred Osim na siyasa da kuma majalisa; sai  Mark Obi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a.
Fushin gwamnan bai tsaya nan baya ya  shafi sauran irin su Francisca Nkoyo Effiom, ma’aikatar kula da bayar da rance,  da  Misis Johnson Ebokpo, ma’aikatar kula da kungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Sauran su ne  Odo Effiong, na ma’aikatar sadarwa da bayar da bayanan fasahar zamani;  Farfesa Temple Edim, na tsare-tsare da ayyukan raya kasa;  sannan kuma sai Eja Dons, na sashen kula da ayyuka tare da bayar da su; sai kuma Ntufam Odo Oji, na ma’aikatar kula da albarkatun gandun daji.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin wadanda abin ya shafa, amma kowanne da jin abin da ya kasance masa, sai ya kaurace wa ofishinsa, su kuma sakatarori sun ce ba su da ikon cewa uffan domin su ma a rubuce aka ba su, ba su da wata masaniya bare su ce kala.