Gwamna M.A. Abubakar ba ya gaba a siyasa – Alkasim

Mai tallafa wa Gwamnan Jihar Bauchi kan al’amuran kafafen watsa labarai na zamani, Malam Muhammad Alkasim, ya ce Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ba ya gaba a harkokin siyasa, kuma hakan ne ya sanya abokan hamayyarsa da dama suke dawowa su rufa masa baya. Muhammad Alkasim ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya […]

Gwamna M.A. Abubakar ba ya gaba a siyasa – Alkasim

Mai tallafa wa Gwamnan Jihar Bauchi kan al’amuran kafafen watsa labarai na zamani, Malam Muhammad Alkasim, ya ce Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ba ya gaba a harkokin siyasa, kuma hakan ne ya sanya abokan hamayyarsa da dama suke dawowa su rufa masa baya.

Muhammad Alkasim ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Bauchi, inda ya ce, Gwamna Abubakar mutum da bai dauki siyasa a matsayin wata aba ta cin mutuncin jama’a ba, kuma bai dauki siyasa a matsayin ko a mutu ko a yi rai ba. “Gwamna Mohammed Abubakar ya dauki siyasa kamar neman aure ne, dole mutum daya ne zai samu nasara, don haka idan aka kammala zabe, maganar ci gaba da adawa ta kare. Zafin kai da adawar siyasa da kuma kyashi su suke kawo cece-ku-ce a siyasa. Bai kamata mutane su rika mancewa da Allah ba, saboda sun fadi a zabe, idan aka yi zabe a koma a tallafa wa wanda ya samu nasara a taru a yi aiki tare don ci gaban jiha da kasa baki daya,” inji shi.

Mai tallafa wa Gwamnan ya ce, idan ’yan siyasa suka cire kyashi kuma suka yarda cewa Allah Yake bayar da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya so, suka dawo suka ba da shawara da gudunmawa ga wanda ya yi nasara a zaben fid-da-gwani ko na gama-gari za a cimma nasara a dukan matakai.

Ya ce “Muna da yakinin cewa Gwamna Mohammed Abubakar zai koma kujerar mulkin Jihar Bauchi, don haka abin da muke fata dukan abokan takararsa da wadanda suka fadi a sauran zabubbukan fitar da gwani su zo su mara masa baya wajen ciyar da Jihar Bauchi gaba.”

Ya ce, zabubbukan cike gurbi da aka gudanar a jihar na kujerun Sanata da dan Majalisar Wakilai da Jam’iyyar APC ta lashe a baya-bayan nan sun nuna cewa jama’ar jihar suna tare da Gwamnan da Jam’iyyar APC, kuma tunda su ne alkalai ya kamata sauran ’yan siyasa na Jam’iyyar APC da sauran jam’iyyu su rika bai wa gwamnatin jihar goyon baya don sauke nauyin da yake kanta. “Jihar Bauchi jiharmu ce baki daya da mu da muke da gwamnati da wadanda suke adawa, wajibi ne mu hada hannu mu gina ta, babu wanda zai zo ya gina mana ita a lokacin da muka ci gaba da hayaniya da hamayya marar amfani,” inji shi.