Gwamna ma ya taba cin bashin mai shayi – Sakataren kungiyar masu shayi

Sana’ar Shayi da Burodi dai dadaddiyar sana’a ce da ta shahara sosai, musamman ma yankunan Arewacin kasar nan. A lokuta da dama, masu sana’ar na matukar taimakawa ta fuskar habakar tattalin arzikin kasa, sakamakon yadda suke huldar kasuwanci da masu gidajen gasa burodi da manyan dillalan kayan hada shayin. Suna kuma taimakon kansu da kansu, […]

Gwamna ma ya taba cin bashin mai shayi – Sakataren kungiyar masu shayi

Sana’ar Shayi da Burodi dai dadaddiyar sana’a ce da ta shahara sosai, musamman ma yankunan Arewacin kasar nan. A lokuta da dama, masu sana’ar na matukar taimakawa ta fuskar habakar tattalin arzikin kasa, sakamakon yadda suke huldar kasuwanci da masu gidajen gasa burodi da manyan dillalan kayan hada shayin. Suna kuma taimakon kansu da kansu, wajen rufa wa kai asiri. A hirarsa da jaridar Aminiya, Sakataren Kungiyar Masu Shayi reshen Jihar Gombe, Malam Haruna Salisu Adamu, ya ce sana’ar Shayi da Burodi ta yi masa riga ta kuma yi masa wando.

 

Ko za ka iya gabatar mana da kanka?

Sunana Haruna Salisu Adamu, kuma ni ne Sakataren Kungiyar Masu Sana’ar Shayi da Burodi, wato TABSA, a takaice (Tea & Bread Sellers Association of Nigeria), reshen Jihar Gombe.

Tun yaushe ka ke wannan sana’ar ta shayi?

Yanzu na kai shekara a kalla 20, ina wannan sana’ar.

Wane irin alfanu sana’ar ta ke da shi cikin al’umma?

Lalle san’ ar shayi tana da alfanu da baya misaltuwa cikin al’umma.  Kadan daga ciki: mu masu ciyar da al’ummar ne, kai har ma da aljanu. Don mu ne mu ke hira har karfe daya na dare, kaga ashe muna ciyar da wanda ba ma mutum ba. Sannan muna tara jama’a da yawa a gurinmu, da mu bawa mutum shayi har ya yi santi har ya bamu labarin gurin da yayi sata (in barawo ne) daga nan mu kuma sai mu koma gefe mu sanarwa jami’an tsaro, sai dai ka ga sun kama shi. Ka ga muna taimakawa wajen tsaro a kasa. Sannan mu amintattune a gurin al’umma, don mutum bai taba ganinmu ba, amma sai ka ya aminta da yazo ya dauna y ace a bashi shayi. Mu kadai ne wanda in ka fito da safe ba ka ga teburan masu shayi kamar uku ba su bude ba, dole da ka koma gida kace gari ba lafiya. Saboda mune ke bude gari, kuma mune ke rufewa.

Da akwai wata gajiya da za ka bugi kirjin samu ta dalilin wannan sana’ar?

Kwarai kuwa, na samu gajiyar wannan sana’ar da yawa. Kamar yin karatu ta dalilin sana’ar, na ginawa iyayena gida, na fitar da su daga gidan haya. Ni ma na ginawa kaina gida, na auri mata biyu-na haifi yara biyar, kuma har yandu a ciki mu ke ci mu ke sha. Dan haka ba abin da zan ce sai Alhamdulillah.

Kasancewar ka sakataren kungiya, ko kuna da alkaluman yawan masu sana’ar Shayi da Burodi a jihar Gombe?

A Jihar Gombe a yanzu muna da akalla mutum 2, 863 wadanda suke da rajistar kungiya. Kuma muna cigaba da wayarwa mambobinmu kai wajen muhimmancin kungiya.

Ya za ka kwatanta samun ku, a wannan watan na Ramadan, ganin cewa da yawan kwastominku na azumi da safe?

A gaskiya a wannan lokaci sai dai hakuri. Musamman yadda abin yazo mana, kasancewar an samu hatsaniya a gari (Gombe) har ta kai ga an saka dokar ta baci kwanaki daga karfe shida na yamma duwa shida na safe, har na tsawon mako guda ba ma sana’a, bugu da kari wata ta kare ba albashi, sannan sai ga adumi. Muna samun korafe-korafe na rashin kasuwa a wannan lokaci sai dai addu’a.

Kamar da wane lokaci sana’ar ta fi harka?

An fi samu lokacin hunturu.  A lokacin kaka,  lokacin da amfanin gona ya dawo gida. Sai kuma lokacin sanyi da lokacin damuna. Amma lokacin zafi kam, gaskiya ba ciniki.

Kuma ya danganta da gurin sana’ar mutum, kamar wadanda suke cikin kasuwa nasu da rana ne.  Wadanda suke cikin unguwa, to safe da yamma, sun harka. Sai kuma wadanda suke cikin tasha da makarantan, su 24hrs ne.

An ruwaito ka a wata hira kana cewa kusan kowane dan boko, duk girmansa ya taba cin bashin mai shayi-a lokacin da yake karatu.Ko za ka fayyace mana mene ne kake nufi da haka?

Kasancewar mu ne ake samun abinci a wajenmu da sassafe, to ko dan makaranta ko ma’aikacin gwamnati, da duk wani mai sammako idan yana gudun makara a wajenmu yake karyawa.

To  hakan yakan sa mu saba, ko mutum ba shi da kudi sai ka ga ya zo ya ci bashi. To ka kaddara cikin ’yan makaranta da kake bai wa bashi, za ka samu akwai gwamna, akwai likita, da dan majalisa da soja  da dai sauransu. Ka ga ashe mun taimaka wa gwamna da bashi lokacin da yake karatu. Wadansu kam sai dai ka yafe musu, dan ba biyan mutum za su yi ba.

Mene ne kiranka ga matasa masu raina sana’o’i?

Ina kira da matasa, musamman na jihar Gombe, su bar raina sana’a kowace iri ce, su rike ta su dogara da kansu, kada su sarai da cewa wani zai musu. Yin hakan kan jawo mutuwar zuciya, sai ka ga mutum ya girma bashi da sana’ar yi sai maula. A saboda haka mu rike sana’a komai kankancinta, mu roka gun Allah Zai ba mu.

Ya dangantakarku take da masu gidajen gasa burodi, ganin sana’ar shayi ba ta yiwuwa sai da burodi?

Da ma an ce shayi da burodi. To in ba daya, daya ba zai motsa ba, kuma masu gidajen burodi iyayen gidanmu ne, muna da kyakykyawar fahimta a tsakaninmu.

Wane irin kalubale ke tattare da sana’ar shayi?

Kasancewar mu kananan ’yan kasuwa kuma da ita muka dogara, garancin jari, shi ne babban kalubalenmu, sai ka ga idan za a ba mu bashin kaya sai an mana karin kudi an kure ribarsa. Idan muka sayar sai ka ga dan sauran ribar bai kai mu ci abinci a gida ba kuma ya zama dole. To a haka sai ka ga ka shiga cikin uwar kudi. Da kadan-kadan sai ka ga an biyo ka bashi mai yawa. Har a kai matakin da za a ji ku da mai gidanka, a karshe sai ya rufe ka, Allah Ya sauwake.

Mene ne kiranku ga gwamnati?

Muna kira ga gwamnati, ta taimaka ta shigo al’amarinmu da taimakonta. Mu mutane ne masu yawa, duk kwanar da ka sha za ka same mu kuma muna bada gudummawa sosai akasa, ta fuskar tattalin arziki.  Kuma  abu kadan za ka baiwa mai shayi ya cika masa teburinsa. Don Allah, gwamnati ta waiwaiye mu ta bamu jari muna sayan kaya kudi a hannu-mu bar karban balas a na mana karin kudi.

Ana zargin masu sayar da shayi da amfani da mayen suga cikin shayi, sakamakon tsadar sukari. Me za ka ce kan zargin?

Ba zan musa ba, amma ni kam ban taba gani ba. Kuma akan haka kungiyarmu na ka’idojin da duk wanda aka samu da abinda ya saba ka’ida muna da Kwmitin kula da tsafta da na ladabtarwa, idan muka kama mutum da irin wannan laifi zai sha hukunci. Daga cikin ka’idojinmu akwai:

  1. Ba a shan taba a gurinmu
  2. Ba a yankan farce a gurinmu
  3. Ba a aski a gurin sana’armu.

Kuma idan muka kama da kayan da yayi esfaya, ba za mu bar ka dashi ba.

Ka’idojin suna da yawa, don kula da lafiyar al’umma, kasancewar mu masu ciyarwa.

A baya-bayan nan, an ruwaito kungiyar masu gasa burodi ta kasa ta na gargadin yiyuwar ta kara farashin burodi-sakamakon tashin farashin Fulawa daga Kamfanoni, ya kake ganin hakan zai shafi sana’arku, idan dai karin ya tabbata?

Ba sana’armu kadai ba, duk dan Najeriya saboda duk lokacin da aka ce ka zo sayan abu ka samu an kara kudi ba yadda ka saba saya ba, na farko an rusa maka lissafinka na biyu ranka zai baci. Addu’armu kawai Allah Ya tausaya mana mu talakawan Najeriya Ya ba mu ikon cin jarrabawa don duk wata jarrabawa kanmu take sauka.

Mene ne kiranka ga masu sana’arku da ba su cikin kungiya, wato wadanda ba su yi rajista ba?

Ina kiran dukkan masu sayar da shayi da burodi, ko daga ina yake a a fadin duniya ya do ya yi rajista mu zama tsuntsiya madauri daya

Shiga kungiyar yana da fa’ida sosai, zai kare wa mutum mutuncin sana’arsa, kuma ya kan taimakawa mutum yayinda ya samu jarrabawa kamar an yiwa mutum haihuwa ko zai yi aure ko jinya ko mutuwa ko karayar jari duk muna tallafawa juna.

Kuma yanzu haka ma mun hada kai da kamfanoni suna ba mu kaya daga hannunsu, muna raba wa membobinmu bashi, suna balas mako-mako. Muna karba daga hannun kamfani mu raba wa membobinmu su kawo balas, duk ranar Laraba. Amma muna bai wa mai gaskiya da amana ne kawai.