Gwamna Masari: Akwai gyara a yaki da mugga da jabun magunguna a Jihar Katsina

A sakamakon yadda aka daura damarar yaki da mugga da jabun magunguna a Jihar Katsina, al’amuran da suka shafi harkar lafiya sun gigita kuma sun shiga wani mawuyacin hali a jihar. Dalili ke nan GIZAGO (08065576011) ya bijiro da wannan tsokaci tare da jan hankali tare da ba da shawarwari ga mai girma Gwamnan Jihar […]

Gwamna Masari: Akwai gyara a yaki da mugga da jabun magunguna a Jihar Katsina
Gwamna Masari: Akwai gyara a yaki da mugga da jabun magunguna a Jihar Katsina

A sakamakon yadda aka daura damarar yaki da mugga da jabun magunguna a Jihar Katsina, al’amuran da suka shafi harkar lafiya sun gigita kuma sun shiga wani mawuyacin hali a jihar. Dalili ke nan GIZAGO (08065576011) ya bijiro da wannan tsokaci tare da jan hankali tare da ba da shawarwari ga mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, domin ganin an kawo gyara, yadda al’amarin ba zai cutar da talakawa ba:

A wannan tsokacin, ina son in jawo hankalin mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari dangane da al’amuran sayarwa da tu’ammali da magunguna a fadin Jihar Katsina.
A Juma’ar da ta gabata ce na je hutun mako garinmu Malumfashi, kawai sai na iske wani al’amari mai daure kai, inda na ga shagunan sayar da magunguna da ake kira da kemis-kemis suna cikin rikici. Majiyanci ko da sirinjin allura ya je saye sai ya ga ana ta noke-noke, ana jin tsoron a sayar masa.
Ni kuwa na tambayi dalilin wannan al’amari, sai aka shaida mani cewa wai doka aka kafa, inda jami’an aiwatar da ita suke bi shago-shago suna kwace magunguna tare da kame masu sayar da su. A halin yanzu dai jami’an da aka damka wa tsarin suna haifar da barazana tare da tsoratarwa ga masu kemis-kemis, wanda haka ya ta’azzara al’amuran marasa lafiya a kauyuka da sauran sassan jihar.
Ni kuwa na ce yana da kyau a sake tsari ta yadda za a tantance masu kemis nakwarai da kuma bara-gurbi masu sayar da muggan kwayoyi. Babu wanda zai ki ya ga ana daukar matakan gyara, musamman ma dangane da abin da ya shafi tu’ammali da kwaya, amma dai kam ya zama wajibi a yi dogon nazari ta yadda za a yi gyaran da ya dace, ba gyaran gangar Azbinawa.
Tun da farko, yana da kyau mu sani cewa ba mu da wadatattun asibitoci a Jihar Katsina, musamman ma a kauyuka, inda dakunan shan maganin ba su da yawa kuma babu kwararrun ma’aikata wadatattu. Haka kuma ba mu da isassun likitoci, inda a mafi yawan asinitocinmu, da wuya za ka iske likitoci biyu a lokaci daya suna aiki. Majinyaci sai ya galabaita kafin likita ya zo kansa, koda kuwa lalurar tasa mai bukatar gaugawa ce.
Wadannan matsalolin da sauran makamantansu sun sanya mafi yawan al’umma a birane da kauyuka sun ta’allaka ga kemis-kemis domin samun sauki.
Don haka rana daya a ce za a yi masu fyadar kadanya, abin zai dagula ko ma mu ce ya riga ya dagula al’amura. Wannan matakin zai kara bunkasa matsalar ce, kamar yadda majinyata za su ci gaba da shiga kunci, inda su kuma kwararrun masu gudanar da sana’ar kemis za su shiga matsalar rashin abin yi. Idan aka kai ga wannan yanayin kuwa, babu shakka sai dai du’a’i kawai, domin kuwa sakamakon da hakan zai haifar ba mai dadin ji ba ne.
Da fatan masu ba Gwamna shawara ta fuskokin kiwon lafiya da tsaro za su isar masa da wadannan ’yan shawarwarin, domin a duba yiwuwar kawo gyara a wannan yaki. Shi wannan yaki da jabu ko muggan magunguna, kamata ya yi a faro shi daga tushe, ma’ana a toshe hanyoyin da suke shigowa kasar gaba daya. Ya kamata gwamnati ta dauki matakan tantance kwararrun masu sayar da magunguna a jihar, a ba su lasisi tare da sanya ido sosai wajen gudanarwarsu, yadda ba za su rika sayar da muggan kwayoyi ba. Kuma ya kamata a dauki matakan bincike da tattara bayanan sirri, inda za a rika gano wuraren da ake sayar da muggan kwayoyin, sannan a rika daukar matakan da suka dace, domin kuwa ba kowane kemis ne ke sayar da muggan kwayoyi ba, don haka yi masu kudin goro ba adalci ba ne. Don haka a yi tankade da rairaye, shi ne daidai.
Wani matakin da ya dace kuma gwamna ya dauka, duk da cewa ba na yanzu-yanzu ba ne shi ne, a maida hankali wajen gina asibitoci da dakunan shan magani a sako-sako da lungunan jihar nan, sannan a tanadar masu da isassun ma’aikata tare da bunkasa su da ingantattun magunguna cikin rahusa. Idan aka yi haka, babu shakka za a magance matsalolin jabu ko muggan magunguna; ba tare da an uzura wa talaka ba.
Ba ni kadai ba, shi ma Malam Baba Bala Katsina, wani kwararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya yi dogon sharhi a kafar sadarwa ta Facebook, inda ya ba da shawarwari kan al’amarin.
Kamar yadda ya ce, samuwar kemis-kemis da yawa da wasu wuraren sayar da magunguna alamu ne kawai na cewa lallai akwai matsala a harkar lafiya a jihar, amma abin da ya kamata mu tambayi kawunanmu shi ne, me ya haifar da wannan matsala tun da farko?  
Cikin matsalolin da ya lissafta, sun hada da cewa, akwai rashin wadatattu kuma ingantattun asibitoci da dakunan magani a jihar, don haka idan aka samar da su, yaki da muggan magunguna ba zai yi wahala ba. Shi ma ya kawo shawarar cewa a tanadar da masu farautar bayanai na sirri, wadanda za su rika bankado wurare da kuma masu sayar da jabu ko muggan magunguna, ana hukunta su. Ya ce lallai ne a yi yaki da masu sumoga, wadanda ke shigo da muggan magungunan daga waje. Idan aka datse shigowarsu, babu wani mai kemis da zai samu damar ganinsu, balle ma ya sayar. Kamar yadda ya ce, kashi 70 cikin dari na irin wadannan magunguna, ba a kemis ake sayar da su ba, shi talaka ana amfani da shi ne kawai amma randar na can sama.
Shi kuwa babban malamin jami’a kuma dan siyasa, Malam Ali Muhammad Garba, a ganinsa, cewa ya yi:
Hana sayar da wani jinsi na magunguna, a ganinsa, da an kira masu ruwa da tsaki a lamarin sayar da magani; an sanar da su wannan sabuwar manufa ko tsari (policy) na gwamnati, gwamnati ta yi wa mutane bayani kuma ta wayar wa mutane kai game da wannan tsari.
Ya ce, ya kamata a ce an ba masu sayar da magunguna wa’adi na kamar wata uku, domin su ma su yi shirye-shiryen gyara da neman mafita. A daukar masu alkawari na sayen magungunan da aka haramta masu yanzu, wadanda kuma suke a hannunsu (maimakon kwacewa da ake yi yanzu). Gwamnati ta yi shiri mai kyau na ba da lasisi ga wasu kwararrun masu ilimin magani (Pharmacists) ko makamantansu (pharmacy technicians), domin su sayar da wadannan magungunan. Wannan zai samar wa matasa da suka gama Health Technology da dama aiki.
Ya kamata gwamnati ta yi shiri kuma ta samar da wadannan magungunan a asibitoci domin jama’a su saya. A rika tunasar da mutane ranar da wannan tsarin zai fara aiki sannan idan lokaci ya yi ta aiwatar. Sabanin haka sai kuma a shiga ba mutane hakuri.
Allah Ya kyauta!