Gwamna Masari ya ci a sara masa

Ganin yadda Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya gwammace shiga daji da kansa kuma ya jajanta tare da jajircewa wajen ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo a yankunan da ’yan bidiga suke kai wa hare-hare a jihar ta hanyar tattaunawa da maharan kai-tsaye ya sa nake ganin tattakin da ya yi ya […]

Gwamna Masari ya ci a sara masa

Ganin yadda Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya gwammace shiga daji da kansa kuma ya jajanta tare da jajircewa wajen ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo a yankunan da ’yan bidiga suke kai wa hare-hare a jihar ta hanyar tattaunawa da maharan kai-tsaye ya sa nake ganin tattakin da ya yi ya ci a sara masa.

A halin yanzu jama’a na komawa garuruwansu ba tare da fargaba ko firgici ba. Wadansu ma tuni sun koma gonakinsu da ayyukansu. Mata sun hadu da mazansu sannan yara sun hadu da iyayensu.

Yanzu kuma sai sauraren yadda kowane bangare zai aiwatar da alkawuran da ya dauka don a samu dawwamammen zama lafiya. A tuna da tuntubar juna da zarar an ga wani abu karami ya kunno kai don yin maganinsa.

Sannan daga bisani a san yadda za a bi a karbe dimbin makaman da suke hannun maharan da kuma mutanen gari cikin lalama. Domin in ba a yi haka ba to kuwa akwai damuwa nan gaba domin kamar an kashe maciji ne ba a sare kansa ba. Gwamnati ta yi maganin ’yan caji da beli su kuma alkalai su ji tsoron Allah su rika yanke hukuncin kararrakin da suke a gabansu cikin lokaci da adalci.

Matasa su nemi ayyukan yi don su kauce ma fada wa tarkon Shaidan, su daina jiran sai gwamnati ta sama musu aikin yi. Ya kamata matasanmu su koyi sana’o’in hannu musamman na gyaran wutar lantarki da aikin fulamba da kanikanci da sayar da kayan babur da mota da aikin dab’i da sauran ayyuka ko sana’o’i wadanda idan aka kuskura aka fada cikin lalurarsu a karshen mako musamman ranar Lahadi to kuwa ba za a samu masu yin su ba sai dai ranar Litinin saboda mutanenmu ba sa yinsu.

Iro Surajo Abuja, (0816 343 9197)