Gwamna Masari ya fanshi fursunoni 49 daga aljihunsa

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya fanshi fursunoni 49 da suke zama kaso a gidan kurkuku, kuma ya yi wa fursunoni 18 afuwa don nuna murna da kammala azumin watan Ramadan na bana lafiya. Gwamna Masari ya yi amfani da kudin aljihunsa Naira miliyan daya da dubu 120 wajen biyan tarar da aka […]

Gwamna Masari ya fanshi fursunoni 49 daga aljihunsa
Gwamna Masari ya fanshi fursunoni 49 daga aljihunsa

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya fanshi fursunoni 49 da suke zama kaso a gidan kurkuku, kuma ya yi wa fursunoni 18 afuwa don nuna murna da kammala azumin watan Ramadan na bana lafiya.
Gwamna Masari ya yi amfani da kudin aljihunsa Naira miliyan daya da dubu 120 wajen biyan tarar da aka ci fursunonin tare da ba kowannensu Naira dubu biyar domin yin kudin motar da za su koma gidajensu domin a yi hidimomin Sallah tare da su.
Gwamnan ya biya tarar ce tare da yi wa fursunonin afuwa a lokacin da ya kai ziyarar ba- zata a gidan yarin Katsina a ranar Larabar makon jiya, kwana biyu a kammala azumin watan Ramadan.
Bayan ganawa da fursunonin, Gwamna Masari ya nuna damuwa kan yadda mafi yawan wadanda ake tsare da su a gidan mazan matasa ne, inda ya yi kira su yi watsi da miyagun dabi’un da suke jefa kansu a ciki.
Gwamnan ya ja hankalinsu kan su rungumi zaman lafiya tare da kokarin koyon sana’o’in da za su rika dogaro da kansu wanda hakan zai kawar da su daga aikata ayyukan da za su jawo su ga shiga irin wannan hali.
Fursunoni 18 da Gwamna Masari ya yi wa afuwa an zabo su ne daga gidajen yarin da ke cikin jihar ne bisa lura da irin kyawawan dabi’unsu a yayin da suke zaune a gidan mazan. Fursunonin mafi yawansu za su share shekara biyu zuwa uku ne a gidan yarin, wadanda zuwa ranar yi masu wannan afuwa wasu ba su wuce wata shida su kammala zaman wa’adinsu a gidan ba.
Babbar Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Katsina, Barista Fatima Jibo ta ce, fursunoni 49 da Gwamnan ya biya wa tara sun hada da wadanda matsalar bashi ta kai su gidan maza ko wadanda suka gaza biyan tarar da kotu ta yi musu.
Gwamna Masari ya yi kira ga alkalai su rika gaggauta yanke hukunci a shari’un da ake gabatar musu, kuma ya roki su rage yawan tura masu kananan laifuffuka zuwa gidan yari, wanda hakan ke haifar da cinkuso a gidajen yari.