Gwamna Masari ya tallafawa masu karatun likitanci

Kimanin dalibai 306 na Jahar Katsina masu karatun aikin likita na cikin gida da waje ne suka samu tallafin kudi naira milyan 56 da dubu 826 daga Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Masari don biyan tallafi kashi na biyu na shekarar 2017.  Da yake shaidawa wakilin Aminiya a ofishinsa, Babban Manajan hukumar dake kula […]

Gwamna Masari ya tallafawa masu karatun likitanci

Kimanin dalibai 306 na Jahar Katsina masu karatun aikin likita na cikin gida da waje ne suka samu tallafin kudi naira milyan 56 da dubu 826 daga Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Masari don biyan tallafi kashi na biyu na shekarar 2017. 

Da yake shaidawa wakilin Aminiya a ofishinsa, Babban Manajan hukumar dake kula da asibitocin jahar, Dokta Abduljalil Umar Abdullahi ya ce daliban dake karatun aikin likita ne na ciki da waje ne zasu amfana da wannan tallafi, domin karfafa masu gwiwa a wajen karatun da suke yi. Ya kara da cewa, “saboda irin muhimmanci da kuma kulawa ta musamman da Gwamna Masari ke yi wa batun kiwon lafiya a jahar, baya ga gyaran manya da wasu kananan asibitocinmu wanda kowa ya ga haka a fili, Gwamnan har ila yau ya bayar da umarnin daukar wasu kwararrun likitocin tare da kawo wasu kayan aikin baya ga gyara wadanda suka lalace. 

A yanzu kuma ya biya kudin tallafi ga wadannan dalibai wadanda suka tafi koyon aikin likita anan cikin gida Najeriya da kuma kasashen waje domin kara inganta sha’anin kiwon lafiya a wannan jaha”.

Akan haka ne shugaban ya yabawa Gwamna Masari akan irin wannan namijin kokari tare kuma da cika alkawurran da ya daukar wa al’ummar jahar a wannan bangare. Sai kuma Dokta Abduljalil ya yi kira ga daliban da su kara mayar da hankali a wajen karatun nasu domin ganin cewa sun dawo gida don bayar da tasu gudunmuwar ta fuskar kiwon lafiya.