Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa

Kwamishinan Ayyuka na Jihar Filato, Mista Chris Hassan ya ce daga shekarar 2007 zuwa ta 2011, gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Jonah Jang ta gina hanyoyin mota 32 a sassan jihar.Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce gwamnatin ta kashe sama da Naira biliyan […]

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa

Kwamishinan Ayyuka na Jihar Filato, Mista Chris Hassan ya ce daga shekarar 2007 zuwa ta 2011, gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Jonah Jang ta gina hanyoyin mota 32 a sassan jihar.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce gwamnatin ta kashe sama da Naira biliyan 30 wajen gina wadannan hanyoyi, inda a yanzu haka take yin wasu hanyoyi 25 da aka kiyasta za a kashe Naira biliyan 65.
Ya ce gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Jang daga lokacin da ta karbi ragamar mulkin zuwa karshen wa’adinta za ta kashe Naira biliyan 95 kan gina hanyoyin mota.
Ya ce “Hanyoyin da muka yi sun hada da na Gwamnatin Tarayya wadanda har zuwa wannan lokaci ba a biya mu ba.”
Kwamishinan ya ce sun yi hanya mai tsawon kilomita 5 a kowace karamar hukuma, kuma kudin da aka yi hanyoyin ba kudin kananan hukumomin ba ne, kudin gwamnatin jihar ne. “Kuma mun yi gadojin sama guda biyu a Gada-Biyu da Mahadar Sakatariya a garin Jos. Da yardar Allah za mu kammala wadannan ayyuka kafin nan karshen wa’adin mulkinmu, domin ’yan kwangilar da muka ba su wadannan ayyuka sun tabbatar mana za su kammala ayyukan, kafin nan da farkon sabuwar shekara mai zuwa,” inji shi.
Sai ya musanta zargin da wasu jama’ar jihar ke yi cewa duk ayyukan da gwamnatin ke yi, tana yin su ne a yankin Arewacin Filato da Gwamna Jang ya fito. Ya ce wannan zargi sharri ne na ’yan siyasa, inda ya ce duk hanyoyin mota da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar a lokacin da ya kai ziyara jihar, a yankin Filato ta Tsakiya ne ya yi. Ya ce a yanzu ma ana yin wasu hanyoyi a yankin Filato ta Tsakiya.