Gwamna Nyako ya tsage gaskiya
Editan Aminiya, Gwamna Nyako ya tsage gaskiya ga gwamnoni. Don haka ku isar da gaisuwata da jinjina ga Mai girma Murtala Nyako (Baba Mai mangwaro), bisa wasikar tsage gaskiya da ya aika wa kungiyar gwamnonin Arewa, a kan kashe-kashen da ake mana a jihohinmu. Yanzu a Arewa ba mu da jagora mai kishi, sai Nyako. […]
Editan Aminiya, Gwamna Nyako ya tsage gaskiya ga gwamnoni. Don haka ku isar da gaisuwata da jinjina ga Mai girma Murtala Nyako (Baba Mai mangwaro), bisa wasikar tsage gaskiya da ya aika wa kungiyar gwamnonin Arewa, a kan kashe-kashen da ake mana a jihohinmu. Yanzu a Arewa ba mu da jagora mai kishi, sai Nyako. Muna yi masa addu’a Allah Ya kare shi. Muna fata Wamako da Almakura da Abdul’Aziz Yari za su rufa masa baya. Daga Baban Maryam 08034507166.
Sakonnin waya
Ga Gwamna Nyako
Assalamu alaikum. Aminiya ku isar min da sako ga Gwamnan Adamawa, Murtala Hammanyero Nyako. Batun albashin wata biyu da suka wuce, ko ya sha ruwan Binuwai ne? Daga Adamu S. MAPEO, Jihar Adamawa 09036587342.
Ta’aziyyar ’Yar’aduwa
Shekara hudu da rasuwar marigayi Umaru Musa Yaraduwa. Allah jikan shi da gafara tare da iyayenmu da suka gabata baki daya, Ya sa tamu ta zo a sa’a. Amin. Usman Lawal Shehu Daura.
Gwamnati a daina yaudara
Ko shakka babu wannan matakin da iyalan wadannan mata suka dauka, ba wani tasiri da zai yi, wajen sako masu ’ya’yansu da ’yan bindiga suka sace. Don haka mafita ita ce Gwamnatin Najeriya ta daina yaudarar talakawanta, ta yi maganin wannan matsalar da take neman kassara yankinmu na Arewa. Daga AbdulMalik Sa’idu Mai Biredi, Tsahar Bagu, Gusau, 08069807496
Hattara matasan Kano!
Salam! Don Allah ina so Edita ya ba ni dama na yi kira ga ’yan uwana matasa, musamman a Jihar Kano, inda ya rage ’yan kwanaki a gudanar da zaben kananan hukumomi da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da hayaniya ranar zabe. Yin hakan ba zai haifar mana da da mai ido ba. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya zaba mana shugabanni masu adalci. Daga Aminu Abdu Ba-ka-noma, Sani Mai Nagge, Kano
Ga Edita
Assalamu alaikum. Haba Edita, kamar na yi maka laifi duk sati sai na sayi tes, amma ban gani! Daga Yusuf Abu AbdoulMaleek Angon Khadeejah. 08139618011.
Tir da kama-karya a Kano
Salam Edita! Tir da mulkin kama-kaya da ake yi a Jihar Kano. Wai sa fitilun kan titi shi ne aiki? Ku je ku duba hanyoyinmu na karkara ku gani mana! Misali, hanyarmu mai zuwa sakatariyar karamar Hukumar Bebeji, wacce ta tashi daga Gwarmai zuwa Kofa ta wuce Bebeji. Daga Isyaku Captain Kofa 08114010050.
Ga shugaban karamar Hukumar Tsafe
Assalamu alaikum. Edita na Aminiya ina son a sada min da gaisuwata ga Shugaban karamar Hukumar Tsafe da Gwamnan Jihar Zamfara, Shehi. Allah Ya tsare su. Amin. Daga Kabiru Mu’azu EFCC, Tsafe 07066349673
Soja na cin hanci
Yayin da mu talakawa muke jin sojan Najeriya sun gaza ceto ’yan mata sama da 200, sai ga shi suna karbar Naira 500 a gun fasinja (wurin bincike) da ke kan hanyar Sakkawato. Allah Ka saka mana. Amin. Daga Sani Ya-Malam, Kano 08126466663.
Ga APC Forum
Salam Edita Aminiya, muna godiya ga ’yan kishin jam’iyyar APC Forum, wadda Alhaji Lawal Abubakar baure ke jagoranta. Don su yi magana a kan jama’iyyar APC a Jihar Katsina, saboda rikice-rikicen da suke faruwa a kan zabubbukan cikin gida, don shawo kan lamuran da samun ci gaba a jam’iyyar APC a Jihar Katsina. Daga Zainab Sabo Saulawa, Katsina 08036330102.
Ga ’yan Arewa
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ku fitar da abin da yake mini ciwo a raina. Allahu akbar! ’Yan Arewa mun shiga uku. Ana ta kashe mu. Idan mun kare wa za su mulka? Ga shi dan Zariya ya kasa kare mana mutuncinmu, ballantana ya share mana hawaye. Ka sa a bar mana ’yan mashin su ci gaba da neman abincinsu, ba tare da sun tare hanya ba. Daga Maryam AbdurRasheed 07032366792.
karya na lalata soyayya
Aminci ya tabbata a gare ku. Don Allah a gaya wa samari karya ba abar yi ba ce a gare su, su daina yaudarar kansu da ita domin tana lalata soyayya. Daga Mareeya A.A. Gusau 08064799041.
A yi addu’o’in musamman
Editan Aminiya, zan so in yi kira ga manyan malaman addinan Najeriya, na Musulmi da Kirista da su tashi, su jagoranci addu’o’in musamman kan shigowar Amurkawa da Ingila da China har ma da Isra’ila. Da ma sun ce kasarmu za ta wargaje nan da 2015. Kada su zo su mamaye mu. Daga Sani Homeboy Mani, Jihar Katsina 08152343673.
Direbobi a natsu
Edita ka isar min da sako ga direbobi, kan su rika isowa wurin sauke mutane a hankali da natsuwa, ta yadda ko da wani abu zai tasho, ko hadari, Allah Ya kawo shi da sauki. Ku sani mugun gudu, ko da a kan hanya ne yana haifar da hadari. Da fatan Allah Ya kiyaye hanya. Daga Malam Mai zanen hula, Gololo 08032822433.
Ga goshin jirgi nan
Najeriya guguwar sauyi ta kada. Kwankwaso da Amaechi muna tare da ku. Ga goshin jirgi nan, ga zaki nan! Masu cutar da mutane a kujerar mulki, muna neman taimakon Allah a kanku. Daga Abdulkadir dangoro. 08068541420.
Tutar Jafaru Isa ce
Edita a ra’ayina da fahimtata, daukacin masu neman mulki a Kano, Lawal Jafaru Isa ne zai iya yi wa Kanawa aikin da ya dace. Shi mutum ne nagari mai tarbiyya. Ya yi a Jihar Kaduna, kowa ya gani. Kuma soyayyar da talakawa ke yi masa ba ta neman abin duniya ba ce. Sai mu jarraba shi mu gani! Daga Ahmad Tiga. 08068643445.
Zargi ba mafita ba ce
Duk harin da aka kai a kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, sai a fara wasan nuna dan yatsa ko zarge-zarge. Wani lokaci ka ji APC ta zargi PDP, ko PDP ta zargi APC; wani lokaci kuma ka ji Buhari ya zargi Jonathan, ko kuma Jonathan ya zargi Buhari; wani lokaci kuma ka ji Musulmi sun zargi Kirista ko Kirista su zargi Musulmi. Da haka da haka dai har a shiriritar da maganar, maimakon a hada kai a yi bincike don kawo karshen matsalar. Wannan babban kalubale ne ga mahukunta. Daga Kwamared Kassim Abubakar Gamawa.
Ga Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kokarin bude kafar ganawa tsakanin mabiya addinai. Kuma idan ’yan uwanmu Kiristoci sun aibata mu, mu yi kokarin nuna musu gaskiyar lamari, ta yadda duk wanda ke da batagari a janibinsa zai taimaka wa hukuma wajen ceto kasar nan. An kashe Kirista, an kashe Musulmi a rikice-rikicen kasar nan. Lallai mu ajiye bambance-bamancenmu na son rai, ta yadda za mu shawo kan tabarbarewar al’amuran Najeriya. Don haka hadin kanmu da tattaunawar fahimta da addu’o’in neman agajin Allah, su za su kai mu gaci. Daga Sham’unu Ali Musa Gabari, Matasan Sufaye. 08035837847.
Mu yaki cin hanci da rashawa
Allah Ya kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya, domin shi ya haifar da rashin tsaro; lalacewar ilimi; da rashin aikin yi da aikata miyagun laifuka da sauransu. Daga Abba Salisu Rimi 08037969710.
Ba mu da manya
Assalamu alaikum. Aminiya a gaskiya Arewa ba mu da manyan kasa, masu kishi. A ce duk kisan da ake yi mana a Arewa sun kasa yin wani abu a kai? Duk sun zama ’yan amshin shata. Ina amfanin shugabancin kasa da suka yi a baya? Sai dai kullum a rika kiransu, ana ba su lambobin yabon shirun da suke yi ana kashe ’yan Arewa. Daga Alhaji Sale Zazzaga. Jos, Bukuru 08036345317.