Gwamna Oshiomhole ya shawarci ’yan siyasa su gyara halayyensu
Gwamnan jihar Edo Kwamared Adam Aliu Oshiomhole ya shawarci ‘yan siyasa a jihar da cewa su gyara halyyenu zuwa na kwarai, tare da ayyukansu da suke yi wa jama’a a daidai lokacin da zaben shekarar 2015 ke karatowa. Gwamnan ya yi wannan tsokacin ne a wani taron gangami na jam’iyyar A.P.C. da ya samu halartar […]
Gwamnan jihar Edo Kwamared Adam Aliu Oshiomhole ya shawarci ‘yan siyasa a jihar da cewa su gyara halyyenu zuwa na kwarai, tare da ayyukansu da suke yi wa jama’a a daidai lokacin da zaben shekarar 2015 ke karatowa. Gwamnan ya yi wannan tsokacin ne a wani taron gangami na jam’iyyar A.P.C. da ya samu halartar gaggan ‘ya‘yan jam’iyyar da sauran mabiyansu a cikin makon jiya da ka gudanar a Fugar Etsako ta tsakiya Jihar Edo.
Kwamared Oshiomhole ya ce ba dai \dai ba ne a ce ‘yan siyasar kasar nan sun bar ayyuka na kwarai da zai haifar wa kasa alheri da amfani ga jama’arsu a cikin harkan mulkin na dimokuradiyya yana mai cewa, don haka dole mu canja fuskar jam’iyyarmu; dole ne mu gina abin da zai amfani al’ummarmu daga yanzu har nan gaba ta hanyar yin abubuwa na kwarai Hakazalika, gwamnan ya ce ina farin ciki da ganin irin hadin kan da jam’iyyarmu take da shi da kuma karbuwarta ga jama’a. Don haka sai ya kara kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar A. P. C. din da su kasance masu kara ba da hadin kai sosai, tare da goyon baya ga mai takararsu a inuwar wannan jam’iyyar. Kuma sai ya ce ya kamata mu gane mutum daya ne zai tsaya takara, don haka dole mu goya masa baya.
Kuma sai ya ce gwamnatinsa za ta taimaka wa abin da zai kawo ci gaba ga al’ummar Jihar Edo ba tare da yin kasa a gwiwa ba, ko nuna wani bambanci ba, inda ya bada tabbacin cewa raguwar lokaci da zai yi akan kujerar gwamnan jihar zai kara bayar da kyakkyawar kulawa ga irin hanyoyi na kawo ci gaba na zamani, domin amfanin alumman Jihar Edo.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a taron Mataimakin Shugaban jam’iyyar A. P. C. na jihar, Mista Charlton Mugaji, ya ce wannan taro mun shirya shi ne, domin wayar da kan mabiyyan jam’iyyarmu ta A. P. C., inda ya bayyana musu Shugabanni masu tsaya musu takara acikin jamiyyar inji shi’’ kuma wannan taron ya gudana cikin lumana a fugar ta Etsako central jihar Edo.