Gwamna Shema: Daga Sarkin Yakin Hausa Zuwa Sarkin Fulanin Katsina
A ranar Asabar da ta gabata ce al’umma suka taru a fadar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, inda aka gudanar da bikin nadin Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema sarautar ‘Sarkin Fulanin Katsina.’Bayan nadin da aka yi, an kuma gabatar da kasaitaccen biki a Dandalin Kangiwa da ke kusa da kofar […]
A ranar Asabar da ta gabata ce al’umma suka taru a fadar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, inda aka gudanar da bikin nadin Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema sarautar ‘Sarkin Fulanin Katsina.’
Bayan nadin da aka yi, an kuma gabatar da kasaitaccen biki a Dandalin Kangiwa da ke kusa da kofar Soro, fadar Sarkin Katsina, inda iyali, ’yan uwa da abokan arziki suka karrama gwamnan ta hanyar shagulgula daban-daban.
A jawabinsa jim kadan da kammala nadin, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, kira ya yi ga gwamnonin kasar nan baki daya da kuma sauran masu rike da madafun iko da su rika nuna adalci ga al’ummar da suke mulka a kowane lokaci.
Sarkin ya kara da cewa, mafi dacewar hanyar magance matsalolin jama’a ita ce ta yin mu’amala da su. “Ba za ka iya taba sanin matsalolin talakawa ba har sai ka kusance su kuma ta wannan hanya ce kawai za ka iya magance musu matsalolinsu.” Kamar yadda sarkin ya bayyana.
Da yake magana game da sarautar ‘Sarkin Fulanin Katsina’ da ya nada Gwamna Shema, sarkin ya ce gwamnan ya cancanci sarautar, musamman ta la’akari da gagarumin aikin da yake yi na bunkasa Jihar Katsina.
“Ilimi kyauta ne ga al’ummar Jihar Katsina, ga kuma yadda a yanzu haka yake ci gaba da bunkasa harkokin noma a jihar. Misali ma, ga tsarin noman rani na ‘Songhai.’ Ya samar da tsangayar koya wa matasa sana’o’in hannu. Wannan ya nuna cewa lallai Jihar Katsina na samun romon dimokradiyya.” Inji sarkin na Katsina.
Haka kuma ya shawarci gwamnan da ya kasance mai hakuri da kuma yin taka-tsan-tsan da kuma nuna tsoron Allah ga dukkan al’amuran da yake aikatawa.
Da ya juya wajen dimbin al’umma da suka halarci bikin nadin, sarkin ya bukace su da su ci gaba da addu’a domin ganin cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo ga kasar nan, kamar kuma yadda ya nemi shugabannin al’umma da su rika yin mulki bisa koyarwar littattafan addini.
A nasu bangaren, shugabannin kananan hukumomin jihar na riko su 34 da suka hada da Alhaji Hussaini Dambo na Ingawa da Mansur Rabi’u Shehu na Malumfashi da Mansur Usman Murnai na Kusada da sauransu, baya ga halartar bikin nadin da suka yi, sun kuma sayi shafi ne na musamman jaridar ‘Sunday Trust’ inda suka taya gwamnan murna.
Kamar yadda suka bayyana a shafin da ke dauke da sa hannuwansu: “Wannan muhimmiyar sarauta da ma wasu da dama da aka nada shi a wurare daban-daban, girmamawa ce da ta dace da kai, kuma alama ce da ke nuna irin gagarumin aikin bunkasa al’umma da kake yi a jiharka.”
A halin da ake ciki, Gwamna Shema na rike da sarautun gargajiya guda uku ke nan, wadanda suka hada da ‘Sarkin Yakin Hausa,’ wadda Sarkin Daura ya nada shi da sarautar ‘Atta Oja Igala,’ wacce Atta na Igala ya nada shi, sai kuma ita wannan ta ‘Sarkin Fulanin Katsina’ da Sarkin Katsina ya nada shi.
Ko yaya al’umma ke ganin dacewar Gwamna Shema da wannan sarautar? Malam Hassan Nagado, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce: “Masarautar Katsina ta kyauta da ta nada shi wannan sarauta, domin ya cancanta. Masarautar ta yi la’akari da dimbin ayyukan raya kasa da gwamnan ya aiwatar a tsawon mulkinsa na shekara shida, su suka ja hankalin majalisar sarki har ta yi masa wannan karramawar a matsayin jigon zaman lafiya da ci gaban al’umma. Sannan ayyukan raya kasa da gwamnan ya gudanar a cikin al’ummomi, musamman a kauyukan Fulani, su suka sanya majalisar Sarki ta aminta da shi. Kuma ayyukan kula da lafiyar al’umma, musamman tsarin kula da lafiya na tafi-da-gidanka, wanda ake bibiyar dimbin Fulanin da ke fadin jihar sun dauki hankalin sarki.”
An haifi Gwamna Shema a ranar 22 ga Satumbar 1957, a garin Dutsin-ma da ke Jihar Katsina. Ya fara karatunsa na firamare a makarantar a 1964, sannan ya samu shiga Sakandiren Gwamnati da ke Kafanchan, inda ya samu shaidar kammala jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC), a 1976. Shema ya halarci Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Zariya, inda ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a tsakanin 1980 zuwa 1983, sannan ya samu halartar makarantar samun horon kwarewa a aikin lauya a 1984. Ya zama Gwamnan Jihar Katsina ne tun daga 2007, inda aka sake zabensa a karo na biyu a 2011, bayan ya kammala wa’adinsa na farko.
Wasu daga cikin muhimman mutanen da suka halarci bikin nadin, sun hada da sabon shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Ahmad Mu’azu.