Gwamna Shema ka yi dokar Muradun karni

A daidai lokacin da Gwamnonin Jihohin kasar nan suka fita batun Muradun karni (MGDs), Gwamnatin Shema a Katsina sai fafatawa take yi kan yadda za ta samar da tsaftattacen rowan sha da isassun gidajen kwana da ilimi ga al’umma, amma ba yi wa shirin Shema wata doka da za ta tabbatar da an ci gaba […]

Gwamna Shema ka yi dokar Muradun karni
Gwamna Shema ka yi dokar Muradun karni

A daidai lokacin da Gwamnonin Jihohin kasar nan suka fita batun Muradun karni (MGDs), Gwamnatin Shema a Katsina sai fafatawa take yi kan yadda za ta samar da tsaftattacen rowan sha da isassun gidajen kwana da ilimi ga al’umma, amma ba yi wa shirin Shema wata doka da za ta tabbatar da an ci gaba da kyawawan ayyukan da yake aiwatarwa. A yau dukm mai kishin Jihar Katsina ya san an tagaza kan al’amuran da suka shafi muradun karni, tunda ba a bukatar iyayen mutum su zama ’yan jam’iyya kafin a tura shi kasar waje karo ilimi; ko kauye suna yin Shema, ko ba sa yinsa ana yi musu ayyukan raya kasa da suka dace.
Gwamna Shema da mukarrabanka, tunda ku wakilan al’umma ne, ya zama dole ka sanya a yi dokar cimma murtadun karni, wadda za ta tabbatar da cewa ko da Kansila na karamar hukuma, akwai aikin da zai yi wa al’umma a fagen samar da ilimin Firamare kyauta da kula da lafiya matakin farko, uwa-uba da tsaftar muhalli. Yin haka ya zama dole, tunda akwai wata fada ta Turawa, wai “al’ummar da ke cikin koshin lafiya tana tare da arzikin rayuwa – ko lafiya dukiya ce – ‘health is wealth). Sannan ka yi kokarin ganin an cusa dabarun cimma muradun karni a makarantun Firamare na Jihar Katsina.
Kuma mutane da dama sun karanta a jaridu, cikakkun bayanan da Babban Daraktan Hukumar Samar da Ruwan sha da Tsaftar Muhalli a Yankunan Karkara na Jihar Katsina, Abubakar Muhammed Gege, ya bayyana wa duniya kudurin Jihar Katsina na cimma Muradun karni (MDGs) nan da shkara ta 2015. A cewarsa:
“A zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa, Marigayi, Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa, da ya yi Gwamnan Jihar Katsina ya kafa Hukumar Samar da Ruwan Sha da Tsaftacce Muhalli a Yankunan Karkara, cikin shekarar 2003. A kokarin wannan hukuma na cimma manufofi da nauyin da ya rataya a kanta, dole sai da ta hada kai da sauran sassan ayyuk na gwamnati, kai har ma da kungiyoyin da ba ruwansu da Gwamnati (NGOs). A lokacin da Gwmanatin Shema ta kama ragamar mulki, ta ga irin namijin kokarin da aka yi, sai ta himmatu wajen cimma manufofin hukumar fiye da kashi 30 cikin 100 na abin da ta samu a kasa. Yin hakan y zama dole, musamman ganin cewa kimanin kashi 60 cikin 100 na al’ummomin da ke zaune a yankunan karkara, a kauyukan da ke da mutanen da yawan su ya kai dubu biyar ko kasa da haka, ba su da ruwan sha, ballanta a yi maganar tsaftar muhalli. Don haka a lokacin da aka nada ni Daraktan farko, a shekarar 2007, sai muka inganta daga kashi 45  cikin 100, inda a shekarar 2007 muka kara kokari, har sai da muka cimma gyara da kashi 65 cikin 100, inda yankunan karkara suka samu tsaftattacen rowan sha a shekarar 2009. Sannan a wannan shkarar ta 2014 za mu sake nazarin yawan mutanen kauyukan da ya kamata a warware matsalolin.
Da muka fahimci cewa gurbata ruwan sha, musamman a birane babbar matsala ce ga lafiyar al’umma, sai muka kaddamar da shirin tsaftace muhalli na gama-gari a karshen kowane wata. Sannan muka hada kai da Hukumomin duniya, musamman DFID (Hukumar Raya Ci gaban kasashe ta Birtaniya) da Asusun Raya Ci gaban kananan Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF); sannan wata kungiya da ke yaki da ba-haya a bainar jama’a, har ta kai ga mun samu a kalla kananan hukumomi uku wadanda ba su da matsalar yin ba-haya a filin Allah. Babar manufarmu cimma Muradun karni da kashi 85 cikin 100 nan da shekarar 2015.
Ita kanta uwargidan gwamna, Hajiya Fatima Shema akwai ayyukan sa kai da take yi, musamman na koya wa mata sana’o’in hannu, da shirin fadakarwa kan yaki da cutar yoyon fitsari da shan inna da kanjamu da mai karya garkuwar jiki.
Idan har Gwamnatin Shema za ta iya cimma muradun karni da dama a cikin kankanen lokaci, me zai sanya, al’umma ba za ta yi kokarin ganin a dore da shirin ba? Sai mu bai w akawunanmu amsa, kan yadda muke son ganin masu rike da mukaman siyasa na aiki tukuru.
Aiwatar da ayyukan raya karkara ko ci gaban al’umma, a fannonin da suka shafi ilimi da kiwon lafiya da kula da muhalli, ba hakkin Hukuma ita kadai ba ce, har ma kowane dan jiha yana da rawar da zai kada. Don haka muke ganin idan har Gwamna Shema yana sona mutanen Jihar Katsina su tabbatar da cewa shi mai kaunarsu ne, to ya yi dokar cimma muradun karni, wadda za ta samu amincewar majalisar jiha, tare da daukacin al’umma. Yin haka zai bayar da dama mai mulki a wannan jiha tamu, ya rika aiwatar da managartan ayyuka, don amfanin al’umma.
Ina mai kyautata zaton da zarar Gwamna Shema ya sanya an yi doka game da aiwatar da muradun karni a Jihar Katsina, tabbas, al’ummar jiharmu za su rika yi wa ’yan siyasa barazana, ta yadda duk mai son komawa kan kujerar wakilcin al’umma, dole sai ya nuna irin gudunmuwarsa a fannonin kula da lafiyar mata masu juna biyu da kanana yara; da tsaftar muhalli; da samar da gidajen kwana, musmaman ga ma’aikata a yankunan karkara.
Idan Jama’ar jiharmu suka taimaka aka yi wannan doka ta muradun karni, za mu rage yawan mabarata da matasa masu zaman kashe wando, ta yadda ’ya’yanmu za su kasance a cikin makarantun koyon ilimi ko na sana’a.
Babbar fa’idar yin wannan doka ta muradun karni, it ace ayyuka managarta da Shema ya fara za a ci gaba koyi wajen aiwatar da su, sannan ma’aikatan kananan hukumomi za su samu ayyukamn yi a kullum. Lallai lokaci ya yi da za a duba yiwuwar yin dokar cimma muradun karni a Jihar Katsina.

Baban gado ya rubutio makalarsa daga F/Samji [email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya