Gwamna Shema: Kar ka bata rawarka da tsalle

Makalar tawa ta yau kamar yadda kanunta ya nuna, za ta mayar da hankali ne a kan guguwa da danbarwar siyasar da ake ciki a Jiha Katsina, kamar yadda take kadawa a sauran jihohi dama kasa baki daya, saboda irin yadda kakar zaben shekara mai zuwa take ta kara kamari. Mu a Jihar Katsina, inda […]

Gwamna Shema: Kar ka bata rawarka da tsalle
Gwamna Shema: Kar ka bata rawarka da tsalle

Makalar tawa ta yau kamar yadda kanunta ya nuna, za ta mayar da hankali ne a kan guguwa da danbarwar siyasar da ake ciki a Jiha Katsina, kamar yadda take kadawa a sauran jihohi dama kasa baki daya, saboda irin yadda kakar zaben shekara mai zuwa take ta kara kamari. Mu a Jihar Katsina, inda jam`iyyar PDP ke mulki tun da aka fara mulkin wannan jamhuriyar ta hudu a shekarar 1999. Sa-in-sa ake fama da ita tsakanin daya daga cikin masu neman takarar mukamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar ta PDP, Alhaji Umaru Abdullahi Tsauri, wanda ake yi wa lakabi da TATA da gwamnan jihar Barista Ibrahim Shehu Shema, sa-in-sar da ta kai fagen wasu daga cikin magoya bayan mutanen biyu sun ara, sun yafa, ta yadda kullum kara zafafafa take yi. Kafin in yi nisa, mai karatu ina so in tabbatar maka a cikin rayuwata, sau uku na taba haduwa da Gwamnan jihata Barista Ibrahim Shehu Shema, tun kusan shekaru sha shidda da yake cikin harkokin siyasar kasar nan ta jamhuriya ta hudu da aka fara a shekarar 1999. Na farko a zamansa na Kwamishinan shari`a na jihar Katsina a cikin zango farko na gwamnatin marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa. A lokacin guguwar neman fara aiki da shari`ar Islama tana kadawa a wasu jihohin arewa, musamman na shiyyar Arewa maso Yamma, shiyyar da Jiha Katsina take ciki, a wancan lokacin ina Wakilin sashen Hausa na Radiyon BBC Landan, lokacin da naje Katsina don samu bayanin matsayin gwamnatin jihar na fara aiki da tsarin shari`ar Islama din, inda a lokacin na sadu da shi a ofis dinsa.

Haduwa ta biyu ita ce ta bayan ya bar Kwamishinan shari`a, inda muka hadu da shi ya fito daga wani gidan tuwo a Abuja, babban birnin tarayya, Ni kuma zan shiga, a bisa ga waccan sanayyar farko, ya gane ni na gane shi, don haka muka tsaya muka gaisa, har ya dauko katinsa na Kamfaninsa na aikin Lauya ya ba ni. Haduwa ta uku ita ce wadda muka yi a filin jirgin saman Katsina a rana ta uku da mutuwar mai Martaba Sarkin Katsina marigayi Alhaji Muhammadu Kabir Usman, cikin watan Maris din shekarar 2008, a lokacin da shi da Kwamishinoninsa suke kan layi na ganin sun yi bankwana da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru `Yar`aduwa a lokacin da zai koma Abuja. Ni kuma muna tare da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, kuma Sanata Ibrahim Saminu Turaki a cikin yawon da muka yi da shi a filin, har ya ja ni muka je wurin, a nan ma mun gaisa da Gwamna Shema, har yake tambayar ina ina? Mai karatu ka ga daya daga cikin wadancan haduwa ta aiki ce, biyu kuma hanya ta hada.
Ga abokin cacar bakan Gwamna Shema kuwa, wato TATA Allah Ya sa ni ban taba haduwa da shi ba a rayuwa, ta yadda in ban da a wannan jarida ta makon da ya gabata da na ga hotonsa balo-balo, to kuwa da sai in ce da mai karatu ko da hotonsa ban taba gani ba. Amma dai na fara sanin labarinsa a shekarar da ta gabata ta jarida, lokacin da na karanta labarinsa da yake zargin wasu magoya bayan Gwamna Shema sun kai masa hari a garin danja, Hedkwatar karamar Hukumar danja ta Jihar Katsina, kuma tun a wancan lokacin batun da ake magana, kawo har wannan lokaci shi ne, TATAN yana neman takarar Gwamnan Jihar ta Katsina ne a inuwar jam`iyyarsu ta PDP. Takarar da ta tabbata Gwamnatin Jihar Katsina ba ta kaunarta, bisa ga dalilan da ita kadai ta bar wa kanta sa ni.
A tsawon kusan shekaru takwas da Gwamna Shema yake nema akan karagar mulkin jihar, zuwa yanzu, Ta bakin masu iya magana, “Hasidin-iza-Hasada” kawai zai ce Gwamna Shema bai yi wa mutanen jihar da jam`iyyarsu ta PDP ayyukan ci gaba ba, kama daga fannin ilmi da kiwon lafiya da samar da ruwan sha da gina hanyoyi da samar da ayyukan yi, musamman ga matasa da sauran ayyukan raya kasa. Kuma a dukkan luguna da sako na jihar, da rashin fili ba zai ba da damar in kawo su dalla-dalla ba. Haka labarin yake akan jam`iyyarsu ta PDP, a nan kusa dai ban sa ni ba, kuma banga bare kuma in ji labarin wata jiha da ta gina katafariyar Sakatariyar jam`iyya ta jiha irin ta Jihar Katsina. Dukkan wadannan ayyuka, ta tabbata cewa Gwamna Shema bai ci bashin koda sisin kwabo ba, walau a ciki ko daga wajen kasar nan ba. dukkan ayyukan da ya yi da `yan kudin shigar da ake ba jihar ne da kananan Hukumominta.
Amma sai dai kash! Duk da wadannan nasarori na Gwamna Shema a Jihar Katsina, babbar matsalarsa ba ya iya daure wa adawar cikin gida, kamar yadda tarihi zuwa yanzu ya tabbatar. Mu mutanen Jihar Katsina mun san yadda aka kwashe tsakanin Sanata Lado dan Marke a shekarar 2011, a lokacin da Sanatan ya fito gadan-gadan ya nuna kujerar gwamnan jihar yake so ta kowane hali. Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan kama Sanatan da aka yi aka buga masa ankwa. Ba su daidata ba sai da Sanata Lado ya dawo cikin jam`iyyarsu ta PDP, sannan kuma ya ba da shelar duk magoya bayansa su zabi Gwamna Shema kana suka zauna lafiya. Abokin aikinmu Malam Abubakar Abdurraham Janar Manaja na tashar gidan Radiyon Kwamfaniyan FM ta tarayya, shi ma ba su kwashe da dadi ba da Gwamna Shema a kokarinsa na tabbatar da yin aikin jarida, wajen ba kowa damar fadin albarkacin bakinsa. Kai in gajarce maka labari sai da ta kai ya hada shi da jami`an tsaro na farin kaya, wato SSS, akan su yi masa maganinsa, wadanda bayan sun bincika da suka tarar ba wata ka`idar aiki ko tada husuma a cikin aikin gidan Radiyon, kana suka yi watsi da koken na gwamna Shema.
Mai karatu mu kwana nan sai Allah Ya kaimu mako mai zuwa idan Ya a rama mani lokaci da koshin lafiya sai in dora, akan batun da nike son yi.