Gwamna Shettima ya fadi mai dacin

An kafa kungiyar Gwamnonin Arewa ne a shekarar 2000 domin shugabannin Arewa su samu madogara wacce a bisanta za a dauki matakan da suka fi dacewa don warkar wa Arewar da dimbin matsalolin da suka janyo tsumburewarta, har hakan ya sanya ta kasance koma baya, ana ta kyamarta da kyarar ‘ya’yanta a harkokin mulki da […]

Gwamna Shettima ya fadi mai dacin
Gwamna Shettima ya fadi mai dacin

An kafa kungiyar Gwamnonin Arewa ne a shekarar 2000 domin shugabannin Arewa su samu madogara wacce a bisanta za a dauki matakan da suka fi dacewa don warkar wa Arewar da dimbin matsalolin da suka janyo tsumburewarta, har hakan ya sanya ta kasance koma baya, ana ta kyamarta da kyarar ‘ya’yanta a harkokin mulki da na siyasa. Amma maimakon gwamnonin Arewa su mayar da hankalinsu game da aiwatar da wadancan kyawawan manufofin sai suka bari siyasa ta shiga tsakaninsu, ana amfani da addini da kabilanci don rarraba kawunansu. Hakan ne ya sa suka nisanci jama’arsu, har suka bayar da dama ga makiyan Arewa suka kai ta kasa. Daga nan kuma sai  al’amura suka fi karfinsu, ba su iya tabukawa ko tagazawa don magancewa.
Idan da a ce kawunan Gwamnonin Arewa a hade suke, ai da tun-tuni yankinsu ya yi ban-kwana da wahalhalun da jama’arsu ke fuskanta; da  an rabu da batun almajircin da ya sa ake yi wa ‘yan Arewa wani gani-gani; da kuma an kawar da matsalolin da suka hana Arewa kamo ‘yan kudu a fannoni da yawa. Ana iya cewa babu wani kwakkwaran ci gaban da za a yi tinkaho da shi a yankin. Har gobe ana yi wa talakawan Arewa irin alkawurran da ‘yan siyasar zamanin Sardauna suka yi wa  al’ummar lokacinsu na  giggina hanyoyin mota da samar da ruwan sha da makarantu da hasken wutar lantarki. Idan da shugabannin Arewa da gaske suke yi game da kishin Arewa, suna kuma jajircewa don dora ta bisa turbar ci gaba, ai da yanzu ta yi wa sauran sassan Najeriya fintinkau, ta kasance yankin da ake kekkera motoci da na’urorin kakkafa manya-manyan masa’antun da ke wadata al’umma da kayayyakin da suke kerawa har su fitar ketare don  sayarwa.
Rashin ingantattun shugabanni ne ya sa matsaloli suka yi ta taso wa yankin Arewa, na bana yakan dara na bara, kuma kowacce da irin masifar da take haddasawa,  kuma akan talakawa take karewa. A yanzu haka talauci ya yi wa jama’ar Arewa kanta sa’annan jahilci ya mayar da talakawa matalauta,  amma hakan  bai zame wa gwamnonin Arewa ishara ba, sun kasa gane cewa rarrabuwar kawunansu babbar illa ce ga jama’arsu domin hakan ne ya haddasa tashe-tashen hankula da rashin zaman lumanar da suka mayar da al’ummomin Arewa ramin kura, daga ita sai ‘ya’yanta.
Baicin haka nan sun toshe kunnuwansu, ba su jin koke-koken da jama’arsu ke yi game da barnata masu kasa da ake yi da sunan yaki da ta’addanci da kuma yadda ake sassace masu  dukiya da dabbobi don an mayar da su kidahumai, sa’annan kuma ana ta kwararsu ba kakkautawa a dukkan lokutan da suka gangara yankin Kudanci don fatauci ko dillancin kayayyakin abinci.  Har ta kai ba wani amfanin da suke samu saboda tsananin kankarar da jami’an hukumomi ke yi masu akan hanya da sunan haraji. Sai a yanzu ne wasu daga cikin gwamnonin suke ihu bayan hari, watau tattauna wadannan batutuwan a lokacin da hakan ba shi da wani amfani, domin kuwa aikin Gama ya gama.
A makon da ya gabata ne wasu ‘yan kalilan daga cikin Gwamnonin Arewa suka hallara a Kaduna don nazarin yanayin da yankinsu ke ciki ta fuskokin siyasa da tattalin arziki don a dauki matakan gungura Arewar gaba. Wannan ne kusan karo na farko da gwamnonin suka taba yunkurawa dangane haka, to amma sakacin da suka yi shekara da shekaru wajen tunkarar wadannan matsalolin kai tsaye ya sanyaya masu gwiwa, ba wani abin kirkin da za su iya yi a halin yanzu, domin kuwa wasu daga cikin gwamnonin sun rigaya sun kulla abota da wadanda ke haddasa wa Arewar matsalolin da take kasa tsallakewa. Alal misali, tun yaushe ake fama da matsalolin kungiyar Boko Haram a jihohin Arewa, kuma me gwamnonin yankin suka yi a matsayin gudunmawarsu wajen kawo karshen wannan lamari?
Sai a yanzu ne bayan ‘yan ta’addar sun fi  hukumomin tsaro yawa nunkin-ba-nunki, sun kuma fi su muggan makamai irin na zamani ne sa’annan wasu ‘yan tsiraru cikin gwamnonin za su nuna damuwarsu a taron da aka kira don tattauna wasu batutuwan da suka fi wannan  matsalar muhimmanci a gare su? Sai a yanzu ne gwamnonin za su nuna cewa abin na damunsu, bayan sun gaji da hada kai da masu gallaza wa Arewa?  A bisa gaskiya gwamnonin Arewa na da jan aiki a gabansu wajen hada kansu don su samu sukunin yin magana da murya guda a dukkan al’amuran da suka shafi Arewa, kuma a lokacin da ya dace, ba sai sun jira ‘yan siyasar kudun da ke gara su kamar gare-gare ba don su dauki matakin da zai dace da manufar jiga-jigan ‘yan koren Turawa.  Gwamna Kashim Shettima na Jihar Barno, ya dai rigaya ya yi maganar da ta zame tamkar zarar bunu, domin kuwa ya ce a bisa shugabanni ne, watau gwamnoni da kuma Shugaban kasa,  za a dora laifin gawurtar ayyukan ta’addanci, domin su ne ya kamata a ce tuni sun dage wajen magance bala’o’in da ke ragargaza shiyyar Arewa-maso-Gabas. Gwamna Shettima dai ya yi karfin hali, ya baje gaskiya, ina ma da sauran gwamnonin za su gane, su kuma yi aiki da ita? Ai da ba haka ba.