Gwamna Shettima ya rabawa Civilian JTF kyautar filaye
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a jiya ya gana da mambobin ‘yan kato da gora, watau Civilian JTF, 103 wanda aka horar a matsayin sababbin sojojin Najeriya. A lokacin taron da aka gudanar a Maiduguri Gwamnan ya tabbatar wa mambobin cikakken hadin kan gwamnati don haka ya umarci Kwamishinan filaye na jihar da ya baiwa […]
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a jiya ya gana da mambobin ‘yan kato da gora, watau Civilian JTF, 103 wanda aka horar a matsayin sababbin sojojin Najeriya.
A lokacin taron da aka gudanar a Maiduguri Gwamnan ya tabbatar wa mambobin cikakken hadin kan gwamnati don haka ya umarci Kwamishinan filaye na jihar da ya baiwa kowan ne mamba fili. Kuma za a basu tallafin kudi da kayan abinci.