Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa
Cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin akwai tsoffin ’yan majalisar dokokin jihar guda biyu da tsoffin kwamishinoni shida da kuma mata uku.
![Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/01/Gwamna-Abdullahi-Sule-e1735934471924.jpg)
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa.
Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku.
Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon gobe domin tantance su.
Jerin zaɓaɓɓun kwamishinonin sun haɗa da Yakubu Kwanta daga Ƙaramar Hukumar Akwanga sai Tanko Tunga daga Ƙaramar Hukumar Awe da Munirat Abdullahi da Gabriel Agbashi duk daga Ƙaramar Hukumar Doma.
Akwai kuma Barista Isaac Danladi-Amadu daga Ƙaramar Hukumar Karu da Princess Margret Itaki-Elayo daga Ƙaramar Hukumar Keana da Dokta Ibrahim Tanko daga Ƙaramar Hukumar Keffi LGA da kuma Dokta John DW Mamman daga Ƙaramar Hukumar Kokona.
Sauran sun haɗa da Aminu Mu’azu Maifata da CP Usman Baba mai ritaya daga Ƙaramar Hukumar Lafia. Sai Mohammed Sani-Ottos daga Ƙaramar Hukumar Nasarawa da Mohammed Agah-Muluku daga Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon da Barista David Moyi daga Ƙaramar Hukumar Obi.
Sai kuma Dokta Gaza Gwamna daga Ƙaramar Hukumar Toto da Barista Judbo Hauwa Samuel da Muazu Gosho duk daga Ƙaramar Hukumar Wamba LGA.
Aminiya ta lura cewa cikin jerin zaɓaɓɓun kwamishinonin 16 akwai tsoffin ’yan majalisar dokokin jihar guda biyu da tsoffin kwamishinoni 6 da kuma mata uku.