Gwamna Tambuwal ya kashe wa musakai Naira miliyan 400 a wata biyar – Maidoki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kashe sama da miliyan 400 a wata biyar da suka wuce don inganta rayuwar musakai a jihar. Shugaban Kwamitin Zakkah da Wakafi na Jiha Alhaji Lawal Maidoki ya furta haka a taron musakai da aka gudanar a harabar ofishin Zakkah na Jiha a Ranar Musakai ta Duniya […]

Gwamna Tambuwal ya kashe wa musakai Naira miliyan 400 a wata biyar – Maidoki
Gwamna Tambuwal ya kashe wa musakai Naira miliyan 400 a wata biyar – Maidoki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kashe sama da miliyan 400 a wata biyar da suka wuce don inganta rayuwar musakai a jihar. Shugaban Kwamitin Zakkah da Wakafi na Jiha Alhaji Lawal Maidoki ya furta haka a taron musakai da aka gudanar a harabar ofishin Zakkah na Jiha a Ranar Musakai ta Duniya da Majalisar dinkin Duniya ta kebe a makon jiya.
“Gwamnan Sakkwato a wata biyar ya kashe sama da miliyan 229 kan matsalolin musakai da mabukata da wasu miliyan 200 ga marasa lafiya da nakasassu da suka hada da guragu da kutare da makafi da masu ciwon hauka da farfadiya da ke jinya a asibitoci daban-daban na jihar. A gudunmawar da gwamnati ta ba mu a bara, mun yi wa masu tabin hankali dubu bakwai magani, inda muka kwantar da mutum 600 a asibitin Kware. Yanzu haka muna da sunayen mutum 85 da ke da lalurar hauka da ciwon farfadiya da zarar mun kammala tattara sunayen masu lalurar za mu kai su asibiti, don su karbi magani,” inji Maidoki.
Da ya juya kan musakan, ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah su daina yin bara a tituna da shagunan mutane, saboda gwamnati ta hana su kuma tana kokarin tallafa musu a kowane wata. “Ya kamata  su kalli wasu jihohin da ba a tallafa wa gajiyayyu, amma an hana su bara, kuma sun hanu balle nan da aka tallafa masu,” inji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta gyara wurin koyon sana’a na musakai da ke  Kalambaina, saboda kai duk wani mabaraci can a killace shi, sai ya koyi sana’ar da za dogara da ita. Ya yi kira ga masu hannu da shuni su tallafa wa kwamitinsu da kudi, saboda aikin ya yi wa gwamnati yawa. Ya  yi godiya ga Farfesa Arabu Shehu kan gudunmuwar da ya bayar ga kwamitin da fatan wasu za su koyi da shi.