Gwamna Tambuwal ya nemi a hada karfi a magance Boko Haram
Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Animu Waziri Tambuwal ya ce dole ne jama’ar kasar nan su tashi tsaye kan ’yan Boko Haram. “Ba zai yiwu mutanen kasar nan su zura wa mayakan Boko Haram ido ba suna sanya turaddadi da rashin yarda a tsakaninsu ba, wanda hakan ne ya kawo sukurkucewar fahimtar juna ga mabambantan addinai […]
Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Animu Waziri Tambuwal ya ce dole ne jama’ar kasar nan su tashi tsaye kan ’yan Boko Haram.
“Ba zai yiwu mutanen kasar nan su zura wa mayakan Boko Haram ido ba suna sanya turaddadi da rashin yarda a tsakaninsu ba, wanda hakan ne ya kawo sukurkucewar fahimtar juna ga mabambantan addinai da kabilun Najeriya. Yanzu lokaci ne da shugabanni za su yi hobasar ganin sun kawo ci gaban da zai kara tsayar da kasar nan.” Inji Tambuwal.
Gwamnan na Sakkwato ya yi wadannan kalamai ne a ranar Talatar da ta gabata, wajen bikin bude Sakatariyar Cocin Katolika da ke cikin tsakiyar birnin Sakkwato, wadda hukumar gudanarwar Katolika a jihar ta gina don aikace-aikacen mabiya darikar.
Ya kara da cewa hadin kan kasar nan yana dada sukurkucewa tun lokacin da Boko Haram ya tsira, sai dai wannan matsalar girmanta ya danganta da inda kake a cikin kasa. Ya ce dukkan ’yan Najeriya dole ne su sanya kishin dorewar kasa kafin kowace bukata saboda in ba zaman lafiya a kasa ba za a samu damar gudanar da addinin ba.
A jawabinsa wurin bikin, babban bako, Janar T. Y. danjuma, ya ce yakar Boko Haram ga ’yan Najeriya ba karamar wahala ke gare shi ba, sai dai kawai a tunkari kalubalen don samun nasara irin wadda aka yi yanzu ta kwato wasu wuraren da suka kama; inda hakan ya sanya suka canja lalensu ta hanyar shigowa cikin al’umma don cin ma burinsu.
Ya ce sabbin dabarun da suke fitowa da su ba yana nuna karfinsu da kaifin tunaninsu da gwanewarsu ba ne, sai dai yakan nuna jajircewarsu ga bukatarsu ta sanya dubarun zamani fiye da jami’an tsaron Najeriya.
Ya ci gaba da cewa nuna bambancin addini yana daya daga cikin abin da ke wahalar da kasar nan, wanda matukar ba a shawo kansa ba, kasar za ta ci gaba da shan wuya ta wannan bangaren, kuma dole ne mutanen kasar nan su ta shi tsaye ga yakar masu tada kayar baya.
“A lokacin da ’yan Boko Haram suka kira kansu masu kare addini, Shugaba Buhari ya karyata su. Hakan ya dace kowane dan Najeriya ya yi, wato na yin tir ga Boko Haram,” inji shi.