Gwamna Tambuwal ya nemi ma’aikatu su ba majalisa hadin kai

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar su ba da hadin kai ga Majalisar Dokokin Jihar kan duk wani bayani da ta bukata don ciyar da jihar gaba.Gwamnan ya bayyana haka ne a zauren majalisar lokacin kaddamar da kananan kwamitocin majalisar, “Na umarci duk wata ma’aikata ko […]

Gwamna Tambuwal ya nemi ma’aikatu su ba majalisa hadin kai
Gwamna Tambuwal ya nemi ma’aikatu su ba majalisa hadin kai

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar su ba da hadin kai ga Majalisar Dokokin Jihar kan duk wani bayani da ta bukata don ciyar da jihar gaba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a zauren majalisar lokacin kaddamar da kananan kwamitocin majalisar, “Na umarci duk wata ma’aikata ko hukuma ko wani bangare na jihar nan su bai wa Majalisar Dokokin Jihar hadin kai kan duk abin da suka bukata,” inji shi.
Gwamna Tambuwal ya yi alkawarin hada hannu da duk bagarorin gwamnati wato majalisa da bangaren shari’a don kawo wa jama’ar jihar ci gaba ta yadda hadin kai zai ci gaba da wanzuwa tsakaninsu su rika aiki tare ba da gajiyawa ba.
Gwamnan ya ce kofarsa za ta kasance a bude ga dukkan ’yan majalisar 30 a kugiyance ko a daidaiku a duk lokacin da suke bukatar ganinsa.
Shugaban Majalisar Alhaji Salisu Maidaji Gada, bayan kaddamar da kwamitocin ya bayyana cewa aikinsu ne kula da harkokin majalisa don haka kowane kwamiti ya dage don samar da adalci da aiki tukuru da za su taimaki gwamnati a kawo ci gaba ga al’umma.